Dangote vs NMPRA: Majalisar Dattawa Za Ta Bankado Masu Shigo da Gurbataccen Mai
- Majalisar dattawa ta ɗaura ɗamarar fallasa masu yi wa masana'antar man fetur zagon-ƙasa da kuma masu shigo da gurbataccen mai
- Shugaban kwamitin wucin-gadi na bincike kan ɗambarwar man fetur ɗin, Sanata Opeyemi, ya ce dole ne su sauke wannan nauyin
- Opeyemi ya jaddada cewa ba za su ɗagawa kowa ƙafa ba kuma za su yi gaskiya da adalci yayin gudanar da wannan binciken na musamman
Abuja - Majalisar dattawa ta sha alwashin fallasa masu zagon ƙasa ga masana'antar man fetur tare da waɗanda ke shigo da man fetur gurɓatacce a Najeriya.
Kwamitin wucin-gadin na majalisar dattawa na binciken waɗanda ake zargi da zagon-ƙasa ga tattalin arziki a masana'antar mai ta bayyana hakan a ranar Alhamis.
Sanatoci za su binciki dambarwar mai
Shugaban kwamitin, wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, ya karanta takardar ga manema labarai, jaridar The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Bamidele ya ce:
“Za mu ɗauki tsatsauran matakai domin shawo kan manyan matsalolin da za su zama barzana ga tattalin arziki da lafiyar jama'a a ƙasar nan.
“Daga cikin alhakin da ke kanmu, akwai binciko tushen zagon ƙasa ga tattalin arziki a masana'antar man fetur ta Najeriya.
Majalisar dattawa za ta binciki kowa
The Punch ta ruwaito shugaban kwamitin ya kuma ba da tabbacin cewa za su aiki ba sani ba sabo, inda ya ce:
"Kuma za mu karbi duk wasu shawarwari da za su samar da tsaruka mafi kyau a masana'antar tare da bude kofar zuba hannayen jari."
“Mun matuƙar mayar da hankali wurin sauke wannan nauyin. Za kuma mu yi wannan aikin ba tare da tsoro ko yi wa wani alfarma ba.
“Za mu yi adalci ga kowannen ɓangare tare da fatan habakawa da kare martaba da bunkasar tattalin arzikin da ya shafi ƙasarmu ta gado."
Majalisa ta wanke Dangote daga zargi
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta ce binciken da ta yi ya gano cewa dizal da matatar Dangote ke fitarwa ya na da inganci.
Majalisar ta ce ikirari da zargin da NMDPRA ta yi na cewa dizal din Dangote ba shi da kyau karya ne, inda ta ce ya fi wanda ake shigo da shi daga waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng