Gwamna Abba Gida Gida Ya Kai Ziyarar Ba Zata, Ya Daukarwa Mutanen Kano Babban Alkawari

Gwamna Abba Gida Gida Ya Kai Ziyarar Ba Zata, Ya Daukarwa Mutanen Kano Babban Alkawari

  • Gwamnatin Kano ta koka a kan yadda ta samu bangaren ilimi ya lalace a kowanne mataki a fadin jihar tun bayan kama ragamar jagoranci
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana takaicinsa yayin ziyarar ba zata da ya kai wata makarantar mata ta kwalejin kimiyya da fasaha
  • Abba ya ce mutanen Kano su yi hakuri da halin da ilimi ke ciki, kuma sannu a hankali za a gyaran da daliban jihar za su mora

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya roki mazauna jihar su yi hakuri da yadda aka lalata bangaren ilimi a kowanne mataki.

Kara karanta wannan

Kano: An gano kuskuren da zai jefa Abba a matsala a Kano, hadimin Buhari ya ba shi mafita

Abba Kabir Yusuf ya ce idan aka yi hakuri, sannu a hankali gwamnatinsa za ta kawo gyara wanda zai inganta baki daya ilimin jihar.

Abba Kabir
Gwamnatin Kano ta yi alkawarin gyara sashen ilimi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa gwamna Abba Kabir ya ce sun bayyana dokar ta ɓaci a ɓangaren ilimi domin kawo gyara a sashen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun ɗauki matakan gyara makarantu," Abba Gida Gida

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fitar da matakai daban-daban da za su kawo gyara a sashen ilimi.

Gwamnan ya fadi haka ne a ziyarar ba zata da ya kai kwalejin kimiyya da fasaha ta mata da ke kofar Nassarawa a jihar, tare da ɗaukar alkawarin kawo gyara.

Daga cikin matakan da gwamnan ya lissafa akwai gyara tsofaffin makarantun da ake da su, gina sababbin makarantu, daukar karin malamai da samar da kujerun zama

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

Abba ya fusata da lalacewar makarantu

A baya mun ruwaito yadda gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce bai ji dadin halin da makarantun jihar da sauran bangarorin sashen ilimi ke ciki ba.

Gwamnan ya ce ilimi ya lalace ainun, domin akwai miliyoyin dalibai da ke zaune a kasa babu kujeru, yayin da aka cefanar da wasu makarantun yaran Kano.

Gwamnan ya kara da cewa abin takaici ne matuka yadda aka gano dalibai masu yawan gaske ba sa zuwa makaranta a fadin Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.