Zanga Zangar Gama Gari: Direbobin Tankar Fetur sun Fitar da Matsaya a Najeriya

Zanga Zangar Gama Gari: Direbobin Tankar Fetur sun Fitar da Matsaya a Najeriya

  • Kungiyar direbobin tankar fetur da ke karkashin uwar kungiyar ta ma'aikatan man fetur da iskar gas (NUPENG) ta be babu ita a zanga-zanga
  • Wasu fusatattun 'yan kasar nan dai sun shirya fitowa tituna domin zanga-zanga a kan halin da kasa ta tsinci kanta na matsin tattalin arziki
  • Shugaban kungiyar direbobin, Kwamred Augustine Egbon ya ce duk wani direban tankar mai da aka ji zai shiga zanga-zanga ba dan kungiyarsu ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kungiyar direbobin tankar mai ts tsame kanta daga batun shiga zanga-zangar gama gari da wasu 'yan kasar nan su ka shirya gudanarwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tsure, ya bayyana fargabarsa a kan shirin zanga zangar lumana

Fusatattun 'yan Najeriya sun ware ranar 1-15 Agusta, 2024 domin fitowa titunan kasar wajen nuna rashin jin dadin yadda gwamnati ta bar su a cikin wahala.

NUPENG
Kungiyar direbobin tankar fetur sun barranta kansu daga shiga zanga-zanga Hoto: Pius Utomi Ekpei/Bloomberg
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kungiyar PTD, Kwamred Augustine Egbon ya ce su na sane da wasu bata gari da ke son shiga rigar direbobin fetur su yi zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: An samu baraka tsakanin direbobin fetur

Kwamared Augustine Egbon ya fitar da sanarwar barranta kansu daga cikin zanga-zanga biyo bayan rahoton tsohon dan takarar kungiyar, Olaitan Idris ya ce zanga-zanga ba fashi.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Olaitan Idris ya ce zaben da ya samar da Augustine Egbon da Oluchi Chinagorom a matsayin shugaba da mataimaki ba da yawunsu ba ne.

Kungiyar NUPENG ta shiga batun, inda shugabanta, Prince Williams Akporeha ya ce an gudanar da zaben da ya ba wa Kwamred Egbon nasara bisa doka.

Kara karanta wannan

Gwamnonin jihohi 36 sun yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi

Daga bisani Kwamared Augustine ya shawarci'yan jarida su lura da wasu 'yan kungiya marasa manufa mai kyau, inda ya nanata cewa ba za su yi zanga-zanga ba.

Gwamnoni sun shiga taron hana zanga-zanga

A wani labarin kun ji cewa gwamnonin kasar nan sun shiga taro a kan zanga-zanga da 'yan kasar nan su ka ce babu fashi sai sun gudanar daga 1-15 ga watan Agusta.

Gwamnonin na gudanar da taron ne karkashin kungiyarsu ta gwamnonin Najeriya, kuma wannan ne karon farko da su ke taro tun bayan na mafi karancin albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.