Nuhu Ribadu: Gwamnati Za Ta Koma Kotu da Mutane 300 da Ake Zargi da Ta'addanci

Nuhu Ribadu: Gwamnati Za Ta Koma Kotu da Mutane 300 da Ake Zargi da Ta'addanci

  • Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya yi bayani kan yan ta'adda da aka kama a Najeriya
  • Ribadu ya bayyana irin yadda gwamnatin Bola Tinubu ke kokarin ganin an yanke hukunci ga dukkan masu laifin da aka kama
  • Hakan na nuna cewa dukkan masu ta'addanci da aka kama ba za su rika zama a gidajen gyaran hali ba tare da hukunci ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana sabon tsarin gwamnati kan yan ta'addan da suka shiga hannu.

Malam Nuhu Ribadu ya yi bayani ne kan yadda shari'ar wadanda aka kama da laifin ta'addanci za ta rika gudana.

Kara karanta wannan

"Ka tsayar da komai tukun": Sheikh Guruntum ya ja hankalin Tinubu kan halin kunci

Nuhu Ribadu
Gwamnatin tarayya ta canza salon yin shari'a ga yan ta'adda. Hoto: Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mai magana da yawun ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Abu Micheal ne ya bayyana lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a rika shari'ar yan ta'adda

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce za a fara gabatar adadin yan ta'adda masu yawa a gaban kotuna.

Nuhu Ribadu ya ce hakan zai taimaka wajen yin adalci da bayyanawa al'umma yadda al'amuran gwamanti ke gudana.

Rahotan the Cable ya nuna cewa a halin yanzu akwai wadanda ake zargi da ta'addanci sama da mutum 300 a gaban kotuna daban daban.

Yan ta'adda da aka gurfanar a baya

Ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaro ya tabbatar da cewa daga 2017 zuwa 2018 an samu masu laifi mutum 163.

Hala zalika a tsawon lokacin an samu wadanda aka yi musu shari'a amma ba a same su da laifi ba har mutum 882.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

Daga cikin wadanda ba a same su da laifi ba gwamanti ta dauki nauyin koya musu sana'o'i da sauran hanyoyin dogaro da kai.

An mika wadanda aka ceto ga gwamnati

A wani rahoton, kun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya mika mutanen da aka sace a jihar Zamfara ga gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa an mika mutanen a ofishin da ke kula da yaki da ta'addanci karkashin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng