Kasafin N6.2tr: Yadda Tinubu Ware Wa Titin Legas Zuwa Kalaba da Wasu Ayyuka N2trn

Kasafin N6.2tr: Yadda Tinubu Ware Wa Titin Legas Zuwa Kalaba da Wasu Ayyuka N2trn

  • Babban titin Legas zuwa Kalaba da wasu manyan tituna a faɗin ƙasar nan za su laƙume kusan N2trn daga ƙarin kasafin kudin 2024
  • Majalisar tarayya ta amince da kudirin ƙara N6.2trn a kasafin kuɗin kamar yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar
  • Gwamnatin tarayya ta sha nanata cewa an ƙara kuɗin ne saboda sabon mafi karancin albashi da kuma wasu muhimman ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar tarayya ta amince da bukatar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ƙara N6.2trn a kasafin kuɗin 2024 bayan tsallake karatu na uku.

Majalisar dattawa ta amince da kudirin yiwa kasafin garambawul bayan shugaban kwamitin kasafin kuɗi, Olamilekan Adeola (APC, Ogun ta Yamma) ya miƙa rahoto.

Kara karanta wannan

Sakataren Gwamnati ya sa labule da Ministocin Tinubu kan zanga zanga, bayanai sun fito

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Titin Legas zuwa Kalaba da wasu ayyuka za su laƙume N2trn daga kudin da Tinubu ya ƙara a kasafin 2024 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Punch ta ce a ranar 17 ga watan Yuli, 2024, Bola Tinubu ya tura kudirin neman gyara kasafin ga majalisa domin ƙara N6.2trn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ware N2trn domin gina tituna

Bayanan da ke cikin kudirin sun nuna cewa Gwamnatin tarayya za ta kashe kusan N2tn a aikin gina titin Legas zuwa Kalaba da wasu ayyukan tituna a faɗin ƙasar nan.

An gano cewa Tinubu zai kashe N700bn wajen gina titin gabar teku da zai tashi guda.

Wannan titi da ya taso tun daga Legas zuwa Kalaba, ya ratsa ta Ogun, Ondo, Delta, Bayelsa, Fatakwal, Akwa Ibom, zuwa Kuros Riba a Kudu.

Aikin titin jirgin kasa na Fatakwal zuwa Maiduguri zai laƙume N530bn, inda zai ratsa ta jihohin Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Benuwai, Nasarawa, Filato, Kaduna, Bauchi, Gombe, Yobe da Borno.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

Har ila yau, babban titin Trans-Sahara (wanda zai bi ta jihohin Binuwai, Kogi, Nasarawa, Abuja), zai lakuƙe Naira biliyan 200.

Wani bangare a cikin kudirin ya kuma bayyana cewa ayyukan samar da ruwa, da raya madatsun ruwa, da dai sauransu, za su dauki N349bn.

Bugu da ƙari, gwamnatin Bola Tinubu ta ware wa shirin farfaɗo da kiwon dabbobi N75bn, kamar yadda Ripples Nigeria ta rahoto.

Majalisar wakilai ta ƙara kasafin 2024

A nata ɓangaren, Majalisar wakilai ta amince da kudirin neman kara dokar kasafin kudin shekarar 2024 daga N28.7trn zuwa N35.06trn.

A ranar 17 ga Yuli, 2024, Majalisar ta amince da kudirin karin kasafin kudi na N6.2trn da Shugaba Tinubu ya gabatar.

Majalisa ta tsawaita wa'adin kasafin 2023

A wani rahoton kuma majalisar dattawa ta amince da wata bukata da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar mata kan kasafin kudin 2023 da ƙarin kasafin.

Kara karanta wannan

Za a sha jar miya, Tinubu ya fadi yadda zai kashewa 'Yan Najeriya N6.2tn a kasa da wata 6

Shugaba Tinubu ya roki majalisar ta tsawaita wa'adin amincewa da kudurorin dokar kasafin kudin 2023 saboda aiwatar da wasu ayyuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262