NPA: Hukumar Kula da Tasoshin Ruwa ta Tatso Harajin da ya Dara na Kowane Shekara

NPA: Hukumar Kula da Tasoshin Ruwa ta Tatso Harajin da ya Dara na Kowane Shekara

  • Hukumar kula da tashoshin ruwa ta kasa (NPA) ta ce an tattara haraji ga gwamnatin tarayya mai dimbin yawa cikin shekaru uku
  • Tsohon shugaban hukumar, Mohammed Bello Koko ne ya bayyana haka yayin mika ragamar mulki ga sabon shugaban da aka nada
  • Ya ce ana samun karuwar kudin da su ka rika tarawa gwamnati a matsayin haraji, kuma sun tara Naira Tiriliyan 1.423 daga 2022-2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon Manajan darakta na hukumar kula da tasoshin ruwa ta kasa (NPA), Mohammed Bello Koko ya bayyana cewa sun tattarawa gwamnati harajin biliyoyin Naira.

Mohammed Bello Koko ya kara da cewa sun tattara harajin Naira Biliyan 541 a rabin shekara ta 2024.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta yi ram da mai dalilin auren bogi da zargin aikata danyen aiki

Mohammed Bello Koko
Hukumar NPA ta tattara harajin N1.423trn a cikin shekaru uku Hoto: Mohammed Bello Koko
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa hukumar kula da tashoshin ruwan ta mika harajin Naira Miliyan 255 a watannin shidan farko ga asusun harajin hadin gwiwa na CRF.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NPA ta hada harajin N1.423trn a 2022-2024

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Mohammed Bello Koko ya bayyana cewa sun samu karuwar kudin harajin da su ke tattarawa gwamnatin kasar nan.

Ya ce a shekarar 2022 an samu tattara harajin Naira Biliyan 381 kuma an ci gaba da samun karin haraji, inda a 2024 da aka samu Naira Biliyan 541.

Mohammed Bello Koko yayin da ya ke mika aiki, ya bayyana cewa a shekarar 2022 sun tara N381bn, a 2023 kuma sun tattarowa gwamnati N501 , sannan a farkon 2023 sun hado N541bn.

Tsohon shugaban ya ce lissafin kudaden haraji da hukumarsa ta tarawa gwamnatin Najeriya a cikin shekaru uku sun kai N1.423trn.

Kara karanta wannan

Shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina ya fadi illar 'bita da kulli' ga matatar dangote

Hukumar kwastam ta tattara harajin N10.27bn

A baya mun ruwaito cewa hukumar hana fasa kwauri ta kasa ta tattara harajin biliyoyin Naira a cikin watanni biyar - farawa daga watan Janairu zuwa Mayu, 2024.

Shugaban hukumar a Kwara ta shaidawa manema labarai cewa sun yi nasarar samun karinkudin shiga ga gwamnatin tarayya na N10.27bn a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.