Hukumar tattara haraji ta jahar Kaduna ta tara N17bn a wata 6 – shugaban KDIRS

Hukumar tattara haraji ta jahar Kaduna ta tara N17bn a wata 6 – shugaban KDIRS

Hukumar tattara haraji ta jahar Kaduna, KDIRS, ta bayyana cewa daga watan Janairu zuwa watan Yunin bana ta tara kudin haraji daya kai naira biliyan 17 a matsayin kudaden shiga, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Shugaban hukumar, Zaid Abubakar ne ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da majiyar Legit.ng, inda yace kudin da aka samu ya haura kudin da ta yi hasashen samu a cikin watanni 6 da naira biliyan 11.

KU KARANTA: Gwamnan Ekiti ya umarci jami’an gwamnati su dinga magana da harshen Yarbanci

Abubakar ya bayyana tabbacin hukumar za ta tara kudin daya kai naira biliyan 45. “Na tabbatar ma ma’aikatana cewa aiki mukeso, kuma mun basu kwarin gwiwan yin aiki, ina da yakinin zamu cimma manufarmu.

“Mun kammala shirin bin manyan mutane, hukumomin gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu da basa biyan haraji, zamu tabbatar da dukkanin masu biyan haraji sun yi rajista, tare da samun lambar biyan haraji, da kuma tabbatar da sun biya harajinsu a lokacin daya kamata.

“Yin hakan zai kara yawan bayanan masu biyan haraji a jahar, tare da samar da karin kudaden shiga a jahar. Mun samar da ofis a kananan hukumomi domin kula da matsalolin biyan haraji da kuma korafe korafen haraji a matakin kananan hukumomi.” Inji shi.

Daga karshe shugaban hukumar KDIRS ya tabbatar da cewa hukumarsa za ta yi aiki tukuru don ganin duk wanda ya isa biyan haraji ya biya harajin a lokacin daya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel