An Samu Baraka Tsakanin Kwankwaso da Gwamnatin Kano? Gaskiyar Magana Ta Fito

An Samu Baraka Tsakanin Kwankwaso da Gwamnatin Kano? Gaskiyar Magana Ta Fito

  • Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya yi barazanar ɗaukar mataki kan wata jarida
  • Jaridar yanar gizo ta yi ikirarin cewa sau biyu Kwankwaso yana gaza cika sharuddan kwangilolin da gwamnatin jihar Kano ta ba shi
  • Jaridar ta ce, an samu mummunar hargitsi tsakanin Kwankwaso, shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Kwamishinan matasa da wasanni na Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya buƙaci ban hakuri daga 247UReports kan wata wallafarsu ta kwanan nan.

Kwamishinan wasannin, wanda da ne ga Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana zargin 247UReports sun wallafa labarin karyar ne domin ɓata alakarsa da gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP ya 'lakadawa' wata mata dukan tsiya a Kano, an samu bayanai

Mustapha Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan alakarsa da gwamnatin Kano
Mustapha Rabiu Kwankwaso zai yi karar jaridar da ke son bata masa suna a Kano. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Mustapha Kwankwaso ya aika wasika ga gidan jaridar ta hannun tawagar lauyoyinsa, H.M Muhammad & Co, kamar yadda Sanusi Bature Dawakin-Tofa ta wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Nufin bata mani suna aka yi' - Kwankwaso

Kwankwaso ya ce wallafar da da aka yi, ya yi kama da wani shiri na bata masa sunansa wanda ya dade yana ginawa da kuma bata alakarsa da gwamnatin Kano.

A wani labari da 247UReports ta fitar, ta yi ikirarin cewa gwamnatin Kano ta ba Kwankwaso kwangiloli har sau biyu kuma ya gaza cika sharuddanssu.

Bugu da ƙari, wallafar ta zargi cewa an samu sabani tsakanin Kwankwaso, shugaban ma'aikatan Gwamnan jihar Kano da Gwamnan da kansa.

Lauyoyi Kwankwaso sun mika takardar bukata

Lauyoyin kwamishinan matasan, sun aika wasika ga editan jaridar, Ikenna Ellis Ezenkwe suna masu cewa:

Kara karanta wannan

Bello Turji: Gwamnatin Zamfara ta yi martani ga Ministan tsaro, Matawalle bayan ya ba ta shawara

“Bisa ga umarnin da wanda muke wakilta, mun tuntubi ofishin ku game da wani labari da kuka buga a baya-bayan nan wanda ya yi illa ga wanda muke karewa da kuma gwamnatin jihar Kano.
"Waɗannan zarge-zargen da kuka wallafa gaba ɗayansu ba gaskiya bane kuma basu da tushe.
Mista Kwankwaso yana neman bukatar ku rubuta takardar ban hakuri tare da bugawa a jaridu biyu na kasa da kuma biyan diyya a cikin sa’o’i 48 da samun wannan wasika.

Mustapha Kwankwaso zai je kotu

Idan har jaridar ta gaza yin hakan, lauyoyin sun shaida cewa sun samu izini daga Kwankwaso na su dauki matakin shari'a.

Idan wadanda ake tuhuma su ka yi gardama, za a nemi bin kadin batancin da aka yiwa kwamishinan.

Wanene editan jaridar?

Editan shi ne Ikenna Ellis Ezenkwe wanda mawallafin jaridar yanar gizo ne kuma haifaffen jihar Kano ne.

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Dawakin Tofa ya ce ko a baya bayan nan sai da jaridar ta rika buga labarai da nufin bata jami'an gwamnatin jihar saboda rashin samun kwangila.

Kara karanta wannan

"A daina alakanta ni da 'yan bindiga": Matawalle ya yi magana kan bidiyon Bello Turji

Ikenna haifaffen jihar Kano ne a cikin iyalin marigayi Fasto Ezenkwe, mishanari kuma ma'aikacin jami'ar Bayero.

Gwamnatin Kano za ta cigaba da rusau

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano zai cigaba da Rusau ana tsaka da dambarwar sarauta da ake yi a jihar.

Tuni dai 'yan kasuwa dake kan titin Jami'ar Bayero da ke birnin na Dabo suka fara korafi kan wannan rusau ɗin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.