Zanga Zangar Adawa da Gwamnatin Tinubu Ta Gamu da Cikas, Dalibai Sun Janye Jiki

Zanga Zangar Adawa da Gwamnatin Tinubu Ta Gamu da Cikas, Dalibai Sun Janye Jiki

  • A yayin da ya rage saura kwanaki 8 a fara zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, dalibai sun yi magana
  • Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta ce ta nesanta kanta daga wannan zanga-zangar yayin da ta zabi zaman tattaunawa da gwamnati
  • Hakazalika, wasu kungiyoyin dalibai su ma sun ce ba za su shiga zanga-zangar ba domin gudun maimaita abin da ya faru a 2020

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Dalibai daga manyan makarantu a jihar Legas sun nesanta kansu daga zanga-zangar da ake shirin fara gudanarwa daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

An ce za a gudanar da zanga-zangar ne domin ankarar da gwamnatin Bola Tinubu irin wahalar da ake ciki a Najeriya da ta shafi yunwa da tsadar abinci.

Kara karanta wannan

Wasu matasan Arewa sun fadi sharuda 3 kafin janye zanga zangar da aka shirya

Dalibai sun yi magana kan shiga zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu
Kungiyar daliban Najeriya ta fice daga zanga-zangar da za ayi a fadin Najeriya. Hoto: lagosstate.gov.ng
Asali: Twitter

Daliban karkashin kungiyar daliban Najeriya (NANS) a Legas ta ce za ta yi tattaki ne kawai amma ba zanga-zanga ba, inji wani rahoto da aka wallafa a shafin gwamnatin Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legas: Dalibai sun fice daga zanga-zanga

Daliban sun kuma ce tattakin da za su yi zai ba su damar karfafa guiwar Gwamna Babajide Sanwo-Olu, wanda suka ce ya dade yana tallafa masu.

Da suke magana a wani taron manema labarai a jami'ar jihar Legas (LASU) a Ikeja, shugabannin daliban sun ce za su yi tattaki daga 1 zuwa 10 ga Agusta.

Shugabannin daliban sun ce sun zabi kauracewa zanga-zangar da ake shirin yi ne saboda gujewa maimata abin da ya faru a lokacin zanga-zangar #EndSARS” ta 2020.

Dalibai sun zabi tattaunawa da gwamnati

Shugaban kungiyar NANS reshen jihar Legas, Kwamared Lekan Alimi wanda ya yi magana a madadin daliban ya ce sam babu bukatar yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

ANPPD: Kungiyar Afrika ta fada wa masu shirya zanga zanga abin da ya kamata su yi

Kwamared Alimi ya ce maimakon tsunduma wannan zanga-zangar, dalibai sun yanke shawarar zama da gwamnati domin samun maslaha mai dorewa.

Shugaban NANS ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa na ganin cewa dalibai ba su shiga zanga-zangar ba domin gujewa tashin tashinar da ta taba faruwa a jihar.

Kungiyoyin dalibai sun guji zanga-zanga

Kamar yadda rahoton ya bayyana, kungiyoyin dalibai daga manyan makarantun jami'ar ne suka amince da kauracewa zanga zangar, da suka hada da NAUS, NAPS, NFSAN da SUTIS.

Da take magana, shugabar kungiyar NFSAN, Kwamared Titilayo Ekindayo ta ce dalibai mata a jihar Legas ba za su shiga duk wata zanga-zanga da za ta tayar da hankali ba.

Shi ma shugaban kungiyar NALSS, Kwamared Hafiz Olufowobi ya ce Gwamna Sanwo-Olu ya na kokari a Legas don haka babu dalilin su yi zanga-zanga a jihar.

Miyetti Allah ta fice daga zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta aika sako ga 'ya'yanta na cewa ka da su shiga zanga-zangar da ake shirin yi a kasar.

Kara karanta wannan

"Kowa a fusace ya ke": NLC ta ba Tinubu mafita kan shirin zanga zanga

Shugaban ƙungiyar, Abdullahi Bello-Bodejo, ya bayyana cewa babu hannunsu a zanga-zangar inda ya ce tattaunawa da gwamnati zai fi kawo maslaha ga matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.