Harkar Arziki: Kasar Gabon Tana Zawarcin Dangote Yayin da Hukumomin Najeriya Ke Tuhumarsa

Harkar Arziki: Kasar Gabon Tana Zawarcin Dangote Yayin da Hukumomin Najeriya Ke Tuhumarsa

  • A yayin da takun saka tsakanin Aliko Dangote da hukumomin Najeriya ke kara tsamari, Gabon ta aika sakon gayyata ga dan kasuwar
  • Shugaban kasar Gabon Brice Oligui Nguema ya gayyaci hamshakin attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote da ya zuba jari a kasarsa
  • An ce Shugaba Nguema na son Dangote ya gina masana'antun samar da siminti da takin zamani domin bunkasa tattalin arzikin Gabon

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gabon - Shugaban kasar Gabon Brice Oligui Nguema ya gayyaci hamshakin attajirin Afrika Aliko Dangote da ya zuba jari a kasarsa.

A cewar kamfanin Dangote Industries, an bukaci hamshakin attajirin da ya duba yiwuwar hanyoyin zuba jari a harkar siminti da takin zamani.

Kara karanta wannan

Shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina ya fadi illar 'bita da kulli' ga matatar dangote

Kasar Gabon ta aika sakon gayyatar zuba hannu jari ga Aliko Dangote.
Shugaban kasar Ghana ya nemi Aliko Dangote ya zuba jari a kasarsa. Hoto: @DangoteGroup
Asali: Twitter

An wallafa sanarwar wannan gayyatar ne a shafin kamfanin Dangote na X a ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gabon ta mika kokon bara ga Dangote

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Shugaban kasar Gabon Brice Oligui Nguema ya gayyaci shugaban rukunonin kamfanin Dangote, Aliko Dangote da ya zuba jari a harkar siminti da taki a Gabon.
“Shugaban ya bukaci Dangote ya binciko hanyoyin zuba jari a bangaren siminti da takin zamani a kasarsa, musamman samar da takin urea da phosphate.
“Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda kamfanin Dangote zai ba da gudummawar ci gaban tattalin arzikin Gabon ta hanyar kafa masana’antar siminti da takin zamani."

Gabon ta fadi alfanun Dangote a wajensu

Shugaba Nguema ya nuna yakininsa game da yuwuwar haɗin gwiwar, yana mai bayyana ƙudurin Gabon na samar da yanayi mai kyau na saka hannun jari ga dan kasuwar.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPCL, Kyari ya yi zazzafan martani ga Dangote kan kalamansa

Ya kuma yi nuni da cewa, hadin gwiwa da kamfanin Dangote zai kawo gagarumin ci gaba da suka hada da samar da ayyukan yi, da inganta karfin masana’antun kasar Gabon.

Gayyatar da kasar Gabon mai arzikin man fetur ta yi wa dan kasuwar, na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun baraka tsakanin Dangote damanyan jami’an gwamnatin Najeriya

Gwamnati ta fadi matsayin matatar Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta yi ikirarin cewa har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta ba matatar Dangote lasisin fara aiki ba.

Farouk Ahmed, shugaban hukumar NMDPRA, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati, ranar Alhamis din da ta gabata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.