Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara a Kan Boko Haram Bayan Gwabza Kazamin Fada
- Rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara kan yan ta'addar Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Najeriya ta fafata a wani kazamin fada da yan ta'addar kafin samun nasarar
- Har ila yau, rundunar sojin ta samu nasarar ceto daya daga cikin yan matan Chibok da yan Boko Haram suka sace a makaranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da nasarar da ta samu kan yan Boko Haram a jihar Borno.
Cikin nasarar da rundunar ta samu akwai ceto daya daga cikin yan matan Chibok mai suna Ihyi Audu.
Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin Najeriya sun ceto yar Chibok
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Waidi Shaibu ya sanar da ceto yar Chibok mai suna Ihyi Audu daga hannun Boko Haram.
Manjo Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa sun ceto Ihyi Audu ne a yankin Bama bayan sun fafata da yan ta'addar Boko Haram.
'Yar Chibok ta auri 'Dan Boko Haram
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa yan Boko Haram sun aurawa Ihyi Audu wani dan ta'adda mai suna Abu Darda dan asalin jihar Filato.
A yanzu haka an mika Ihyi da ƴaƴanta da wasu mata kimanin 330 da sojoji suka ceto bayan sun yi musayar wuta ga gwamnatin jihar Borno.
Chibok: Gwamnatin Borno ta yi martani
Kwamishiniyar harkokin mata a jihar Borno, Aishatu Shettima ce ta karbi matan a madadin gwamantin jihar Borno.
Aishatu Shettima ta mika godiya ga rundunar sojin tare da cewa za a kula da lafiyar matan da koya musu sana'o'i.
Sojoji sun gano lagon yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana matsalolin da suka dabaibaye harkokin tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya bayyana matsalolin a wani taron jami'an tsaro a birnin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng