Kotu Ta Amince 'Danuwan Yahaya Bello da Ake Zargi da Badakalar N3bn Ya Tafi Kasar Waje
- Dan uwan tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya samu sahalewar kotu domin zuwa neman lafiya a kasar Burtaniya
- Ana zargin Ali Bello da wasu mutane guda uku da karkatar da makudan kudi har N3bn lokacin mulkin Yahaya Bello a Kogi
- Kotun ta ba shi damar fita kasar ketare domin neman lafiya inda ta ce dole sai da koshin lafiya za a tabbatar da lafinsa ko akasin haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba dan uwan tsohon gwamna Yahaya Bello sabon umarni kan shari'ar da ake yi.
Kotun ta ba Mista Ali Bello damar zuwa kasar Birtaniya domin neman lafiya inda ta mayar masa da fasfo da ta kwace a baya.
Hukuncin kotu kan dan uwan Yahaya Bello
Alkalin kotun, Obiora Egwuatu ya ba da wannan umarni a jiya Litinin 22 ga watan Yulin 2024, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkali Egwuatu ya ce masu korafi sun gaza kawo tabbacin zargin cewa wanda ake zargi zai kawo cikas a belinsa da kuma shaidun da aka bayar kansa.
Ya ce babu yadda za a yi Ali ya saba ka'ida bayan cika dukan abubuwan da ake bukata wurin ba da tabbacin dawowa bayan jinya, Tribune ta tattaro.
"Tun bayan ba shi beli, wanda ake zargi bai taba saba ka'ida ba kuma kullum yana zuwa kotu domin halartar shari'a."
"A duka zaman kotu guda biyu da aka yi, wanda ake zargi bai taba saba ka'idar da aka gindaya ba na ba da beli."
- Obiora Egwuatu
Zargin badakala kan dan uwan Yahaya Bello
Alkalin kotun ya ce ya zama wajibi wanda ake zargi ya kasance cikin lafiya kafin yin shari'a da kuma yanke masa hukunci.
Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Ali da wasu mutane uku da zargin karkatar da N3bn a lokacin mulkin Yahaya Bello.
Yahaya Bello ya nemi alfarma a kotu
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya sake gabatar da sabuwar buƙata a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Yahaya Bello ya buƙaci babbar kotun da ta ɗage ci gaba da sauraron shari'ar da hukumar EFCC ta shigar a kansa har sai baba ta gani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng