A Karon Farko, Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Kan Matasa Masu Shirin Yi Masa Zanga Zanga
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi kira ga matasa da su hakura da fitowa zanga-zanga da suke niyya kan yunwa da matsin rayuwa
- Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a Abuja yayin da ya gana da majalisar sarakunan gargajiya ta Najeriya
- Sarakunan gargajiyan sun bayyana cewa duk abinda tattaunawa cikin lumana bai samar ba, tashin-tashina ba za ta samar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci matasa da su hakura da zanga-zangar da suka shirya yi domin nuna adawa da tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatinsa.
An ce Shugaba Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a wata ganawa da ya yi da majalisar sarakunan gargajiya ta kasa a birnin tarayya Abuja.
Zanga-zanga: Tinubu ya gargadi matasa
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kasar ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, wanda ya yi muhimmin kira ga matasan kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya ce:
“Sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin da kasar nan ke fama da shi, an ce wasu masu mugun nufi na hada kan matasa domin gudanar da zanga-zanga.
"Mu dauki darashi daga abubuwan da suka faru a Indiya da Sudan. Mu kasa ce mai mutane sama da miliyan 200, bai kamata mu fuskanci irin wancan halin ba."
Tinubu ya fadi kokarin da yake yi
A cewar shugaban kasar, abin da ake bukata daga ‘yan Najeriya a wannan mawuyacin lokaci shi ne hakuri da jajircewa domin samun nasarar sauye-sauyen.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnati mai ci ta samar da manufofi da tsare-tsare domin magance matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
“Mun sayo motoci masu amfani da iskar gas, mun bullo da tsarin rancen dalibai, da rarraba kayan abinci, da tarakta da aka sayo domin noma, da samar da taki, da sauran su."
- Bola Tinubu.
Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na matuƙar ƙoƙari wurin yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar.
Sarakunan gargajiya sun yi nasiha
Jaridar Blueprint ta ruwaito Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'adu Abubakar III, ya bayyana tattaunawa a matsayin hanya mafi kyau ta shawo kan matsaloli.
"Abin da tattaunawa ba za ta iya shawo kai ba, babu irin tarzomar da za ta iya. Dole ne a fifita samun zaman lafiya a kan komai."
- Inji Mai alfarma sarkin Musulmi.
Hakazalika, yayin jawabi, Ooni na Ife, Dakta Adeyeye Enitan, ya bayyana kishin ƙasa tsakanin 'yan Najeriya a matsayin mabudin kai wa ga cigaba.
"Kishin ƙasa ɗaya yake da haɗin kan ƙasa. Dole ne a hana duk wani yunƙuri na lalata haɗin kan ƙasa."
- A cewar Ooni na Ife.
An damke mai saida rigunan zanga-zanga
A wani labari na daban, mun ruwaito cewa Bashir Yunusa, matashin ɗan kasuwa a Kantin Kwari da ke jihar Kano ya shiga komar hukuma.
An gano cewa, ya wallafa rigar dake dauke da tambarin zanga-zanga wanda matasa ke shiryawa kan yunwa da matsin rayuwa a shafinsa na Facebook.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng