Ana Saura Kwana 10 Ayi Zanga Zanga, Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Kammala Taron AU

Ana Saura Kwana 10 Ayi Zanga Zanga, Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Kammala Taron AU

  • Shugaban kasa Bola Ahmed ya dawo gida Najeriya bayan kammala taron koli na tsakiyar shekara karo na shida na kungiyar AU
  • Rahotanni sun ce Tinubu ya baje kolin ci gaban ECOWAS a fagen yaki da ta'addanci, tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya da sauransu
  • Shugaban kasar ya dawo Najeriya ne yayin da ya rage saura kwanaki 10 a fara zanga-zangar da wasu matasan kasar suka shirya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja daga birnin Accra na kasar Ghana, bayan halartar taron koli na tsakiyar shekara karo na 6 na kungiyar Tarayyar Afirka.

Shugaban kasar ya dawo Najeriya ne ana saura kwanaki 10 a fara zanga-zangar da wasu matasan kasar suka shirya yi domin adawa da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An fadawa Tinubu sirri 3 domin shawo kan talakan Najeriya cikin sauki

Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan kammala taron AU a Ghana
Daga Ghana zuwa Najeriya: Shugaba Tinubu ya dura Abuja bayan kammala taron AU. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Tinubu ya dawo Najeriya bayan taron AU

An ce Shugaba Tinubu, wanda ya bar Accra ya iso filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da misalin karfe 10 na daren Lahadi, in ji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na Najeriya ya samu tarba daga shugaban ma’aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da sauran manyan jami’an gwamnati.

Kasancewar Tinubu ba ya cikin kasar ne mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi a wani taron kaddamar da shirin noma a Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Me Shugaba Tinubu ya ce a taron AU?

A zamansa na kwanaki biyu a kasar Ghana, shugaba Tinubu, ya halarci taron a matsayinsa na shugaban kungiyar ci gaban kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS).

Kamar yadda rahoton kafar labaran Arise ya nuna, shugaban ya bayyana wasu nasarori da kalubalen da kungiyar ta ECOWAS ta fuskanta.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tinubu ya fadi sabon mafi karancin albashi tare da daukar alkawura 3

Ya baje-kolin ci gaban ECOWAS a fagen yaki da ta'addanci, tallafin zabe, hadewar tattalin arziki, ayyukan jin kai, ilimi, lafiya, makamashi, ma'adinai, da noma.

Zanga-zanga ta dauki harama a Najeriya

A yayin da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa ta dauki harama a Najeriya, fitaccen lauya, Abba Hikima ya ce kama matasan da ake yi ba zai zama mafita ba.

Mun ruwaito Abba ya ce jami'an tsaro ba su da girman dakunan ajiye matasan, inda ya nemi majalisar tarayya ta tsige shugaban kasa idan ba zai iya gyara matsalolin kasar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.