Kano: Jami’an Tsaro Sun Cafke Dan Kasuwar da Ke Sayar da Rigunan Zanga Zanga

Kano: Jami’an Tsaro Sun Cafke Dan Kasuwar da Ke Sayar da Rigunan Zanga Zanga

  • Wani ɗan kasuwa Kantin Kwari dake Kano mai suna Bashir Yunusa, ya shiga hannun hukuma kan tallar rigar zanga-zanga
  • Mai magana da yawun hukumar tsaron farin kaya, Peter Afunanya, ya musanta hannun hukumar kan kamen Yunusa
  • Tuni Amnesty International ta saka baki tare da kushe wannan kame da ta kwatanta da take haƙƙin ɗan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Jami'an tsaro sun kama tare da tsare wani ɗan kasuwa a Kano mai suna Bashir Yunusa kan sayar da rigunan zanga-zanga kan matsin rayuwa a Najeriya.

Bashir Yunusa, wanda yake kasuwanci a kasuwar kantin kwari dake Kano, an kama shi a ranar Juma'a, 19 ga Yuli bayan wallafa hajarsa a dandalin Facebook.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wanda ake zargi da 'kitsa' kisan janar na sojoji a Kano

Matsin rayuwa: An damƙe ɗan kasuwa kan saka hoton rigar zanga-zanga. Hoto daga @Yerwaexpress
Matsin rayuwa: An damƙe ɗan kasuwa kan saka hoton rigar zanga-zanga
Asali: Twitter

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Ibrahim Abubakar, abokin Usman, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa jami'an tsaron sun kama abokinsa a cikin kasuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Abubakar ya ce:

“Abokina Bashir Yunusa (Dan Fillo) ɗan kasuwa ne a kasuwar kwari da ke Kano kuma yana da digiri daga jami'ar Al-Qalam a Katsina.
"Jami'an tsaron Najeriya sun kama shi a kasuwa. Ku daure ku yaɗa wannan bayani tare da ambato duk wanda zai iya taimakawa wurin sakinsa. Maraya ne kuma yana da mahaifiya da ta dogara da shi."

DSS ta kama mai saida rigar zanga-zanga?

A yayin da aka buƙaci mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya, Peter Afunanya, da yayi tsokaci kan lamarin, ya musanta hannun jami'ansu a kamen Bashir.

Afunanya ya ce jinginawa hukumar kama matashin abin takaici ne yayin da ya nemi jama'a su yi watsi da hakan.

Kara karanta wannan

Rusau: Ba a gama rikicin sarauta ba, Abba ya dawo da zancen ruguza wasu wurare a Kano

Amnesty International ta kushe lamarin

A martanin ƙungiyar Amnesty International a shafinta na X, tayi kira ga hukumomin Najeriya da su saki Yunusa nan take kuma ba tare da wani sharaɗi ba.

Amnesty International ta ce:

“Amnesty International tayi Allah wadai da kama Bashir Yunusa kan tallata rigunan yaƙi da shugabanci mara kyau a Najeriya.
"Muna kira ga hukumomin Najeriya da su sake shi nan take kuma ba tare da sharaɗi ba. Dole ne a jaddada 'yancin fadin ra'ayi."

Miyetti Allah ta dauki matsaya kan zanga-zanga

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa, kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta bayyana nisanta kanta daga shiryayyar zanga-zanga da za a yi a fadin Najeriya.

Kungiyar ta ce babu mambanta da zai fito domin su sun yarda da sasanci cikin lumana ba wai zanga-zanga da gwamnati ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.