Fulani Makiyaya Za Su Shiga Zanga Zangar Adawa da Tinubu? Miyetti Allah Ta Magantu
- Ƙungiyar Fulani makiyaya ta fadin Najeriya ta bayyana tsame kanta daga shiryayyar zanga-zangar da za a yi a fadin kasar nan
- Shugaban ƙungiyar, Abdullahi Bello-Bodejo, ya bayyana cewa babu hannunsu kuma mambobin kungiyar ba zasu fito ba
- A taron da suka yi a Karu dake jihar Nasarawa, Bodejo ya miƙa godiya ga gwamnatin Tinubu kan kafa ma'aikatar kula da dabbobi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa - Miyetti Allah Kautal Hore, fitacciyar ƙungiyar Fulani makiyaya ta ce mambobinta ba zasu fito zanga-zangar da za a fara daga ranar 1 ga Agustan 2024 ba.
Alhaji Abdullahi Bello-Bodejo da Injiniya Saleh Alhassan, shugaban ƙungiyar na ƙasa da sakataren ƙungiyar na ƙasa suka bayyana haka a taron manema labarai a jihar Nasarawa.
Miyetti Allah ta dauki matsaya kan zanga-zanga
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Bello-Bodejo na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Miyetti Allah Kautal Hore kai tsaye kuma a ƙarfafe take bayyana cewa ba ta goyon bayan zanga-zangar da aka shirya kuma mambobinta ba zasu fito ba."
Alhaji Bello-Bodejo ya jaddada cewa, ƙungiyar ta fi yadda da tattaunawa ta lumana da hukumomi a kan fitowa ƙwai da ƙwarƙwata domin yin zanga-zanga.
Ita dai wannan zanga-zangar kamar yadda rahotanni suka bayyana, za a gudanar da ita ne domin nuna adawa da halin matsin rayuwa da 'yan kasar ke ciki.
An yabawa Tinubu kan ƙirƙirar ma'aikatar dabbobi
A yayin tattaunawa da manema labaran ne kungiyar ta kara yabawa assasa ma'aikatar dabbobi da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi kwanan nan.
Alhaji Abdulkarim Dayyabu, wani mai fashin baki daga jihar Kano ya bayyana wasi-wasinsa kan kungiyoyi da suka kasa bayyana kansu amma suke kira da ayi zanga-zangar.
Alhaji Abdulkarim, yayi kira ga jama'a da su yi haƙuri tare da goyon bayan gwamnati mai ci a yanzu inda yace ana kan ba gwamnati shawara kan lamurran da suka damu 'yan ƙasar.
Zanga-zanga ta ɓarke a Katsina
A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta jihar Katsina.
An gano cewa, masu zanga-zangar sun fito ne kan buƙatar a tabbatar da tsaro a yankunansu sakamakon ƙamarin da lamurran 'yan bindiga yayi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng