Karshen Alewa: Yan Sanda sun Dakume Kwararren Barawo ya na Tsakiyar Sata a Kaduna

Karshen Alewa: Yan Sanda sun Dakume Kwararren Barawo ya na Tsakiyar Sata a Kaduna

  • Wani matashi mai suna Zahradeenee Suleiman ya shiga komar jami'an tsaro a jihar Kaduna bisa zargin sata da balle shago
  • Wani bawan Alah ne dai ya shigar da korafin cewa ana fasa masa shago, kuma bayan jami'an tsaro sun dira ne suka kama shi
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ya ce ana bincike gabanin zuwa kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Dubun wani barawo ta cika yayin da jami'an 'yan sanda su ka yi ram da shi a jihar Kaduna bayan an yi kururuwar sata ga 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kungiyar Amnesty Intl ta caccaki gwamnati kan kama 'dan gwagwarmyan Tiktok

An kama matashin da ake zargi, Zahradeenee Suleiman dauke da makullan ababen hawa akalla guda 30.

Kaduna
An kama matashi da makullai da ababen hawa da ake zargin na sata ne Hoto; Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa nasarar kama Zahradeenee Suleiman ta samu ne bayan wani sun samu korafi da wuri kan cewa ya na can ya na fasa shago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama matashin," Yan Sanda

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya ce bayan samun rahoton ana sata ne jami'ansu su ka dunguma shagon.

A nan kuma kuma aka yi ram da matashi Zahradeenee Suleiman a cikin shagon da ba na shi ba, Peoples Gazette ta wallafa.

ASP Mansir Hassan ya ce kwarya-kwaryar bincike ta kai ga gano makullan ababe hawa akalla 30, ciki har da wadanda ke iya bude kowane irin abin hawa, an kuma gano babura.

Kara karanta wannan

Fasinjoji sun tsallake rijiya da baya bayan tayoyin sama jirgi sun yi bindiga a Adamawa

Kakakin 'yan sandan ya ce yanzu haka ana ci gaba da bincike gabanin gurfanar da matashin a gaban kotu.

'Yan sanda sun kama matashi

A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sanda jihar Ogun ta cafke wani matashi da satar motar surukinsa, har ma ya sayar da ita bisa abin da bai taka kara ya karya ba.

An kama matashi Fatai Sholola mai shekaru 27 bayan ya cefanar da motar mijin 'yar uwarsa, inda aka ce ya sayar a kan N230,000 sannan ya yi yunkurin bayar da cin hanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.