Tsadar Rayuwa: Bayan Ali Ndume, Sanata Ya Kara Cire Tsoro Ya Fadawa Tinubu Gaskiya

Tsadar Rayuwa: Bayan Ali Ndume, Sanata Ya Kara Cire Tsoro Ya Fadawa Tinubu Gaskiya

  • A yayin da al'ummar Najeriya ke kara shiga kuncin rayuwa saboda tsadar kayayyaki, Sanata ya tura sako ga Bola Tinubu
  • Sanata Ahmed Lawan daga jihar Yobe ya bayyana halin da ake ciki a Najeriya da kuma abin da ya kamata shugaban kasa ya yi
  • Haka zalika Sanata Lawan ya yi kira ga sauran shugabanni kan matakin da ya kamata su dauka domin saukakawa talaka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Biyo bayan kalaman da Sanata Ali Ndume ya yi kan tsadar rayuwa, Sanata Ahmed Lawan ya sake magana.

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya koka kan yadda al'ummar Najeriya ke kara shiga tasko saboda tsadar kayayyaki.

Kara karanta wannan

Ndume: Maganar Sheikh Daurawa kan matsawa talaka a mulkin Tinubu ta tada ƙura

Ahmed Lawan
Ahmed Lawan ya yi kira ga Bola Tinubu kan tsadar rayuwa. Hoto: Ahmed Ibrahim Lawan.
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro maganganu da Sanata Ahmed Lawan ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata da wahalar da ake yi a Najeriya

Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa a yanzu haka tattalin arzikin Najeriya na cikin mawuyacin hali.

Daga cikin tarin matsalolin da suka dabaibaye tattalin Najeriya, Sanatan ya ambaci cewa akwai tashin farashin kayayyaki da rashin ayyukan yi wanda hakan ya jefa talakawa cikin wahala.

Maganar Sanata Lawan kan raba abinci

Haka zalika Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa duk da shugaban kasa ya raba abinci tirela 20 ga kowace jiha amma akwai bukatar kari.

Sanata Ahmed Lawan ya kara da cewa gwamnatin tarayya na buƙatar ta kara raba abinci sosai domin kawo sauki ga yan kasa.

Lawan yana so a dafawa shugaba Tinubu

Kara karanta wannan

Abin da ya faru kafin sauke Sanata Ali Ndume daga matsayinsa a majalisar dattawa

A karshe, Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa Bola Tinubu yana bukatar a sanya masa hannu wajen magance tsadar rayuwa a Najeriya.

Ya ce ya kamata shugabanni su ajiye bambance bambancen siyasa da ƙabila su tunkari matsalolin Najeriya domin samar da mafita.

Ndume: Dele Momodu ya shawarci Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya ba Bola Tinubu shawara kan korar Ali Ndume.

Dele Momodu ya fadi haka ne a cikin wata wasika inda ya bayyanawa Bola Tinubu hakikanin halin da mafi yawan talakawa ake ciki a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng