“A Tsige Shugaban Kasa”: Lauya a Arewa Ya Fadi Abin da Zai Iya Kawo Sassauci ga Talaka

“A Tsige Shugaban Kasa”: Lauya a Arewa Ya Fadi Abin da Zai Iya Kawo Sassauci ga Talaka

  • Fitaccen masanin shari'a kuma lauya, Abba Hikima ya yi magana kan matsin tattalin arziki da ya ta'azzara a Najeriya tare da shirin zanga-zanga
  • Abba Hikima ya ce ma damar aka bari matasa suka je bango, to wa'azi ba zai shige su ba, don haka dole a samar da mafita ga talakan kasar
  • A hannu daya kuma, lauyan ya yi kira ga majalisar tarayya da ta yi zama na musamman ta tsige shugaban kasa idan har ba zai iya gyara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Fitaccen lauya daga jihar Kano, Abba Hikima ya shawarci majalisar tarayya da ta tsige shugaban kasa ma damar aka ga ba zai iya ba.

Kara karanta wannan

Kannywood: An gano babban kuskure da Aminu Saira ya tafka a shirin Labarina

Abba Hikima yana magana ne kan halin matsin rayuwa da 'yan Najeriya ke ciki wanda har ta kai ga wasu matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga.

Abba Hikima ya yi magana kan matsin rayuwa da shirin zanga-zanga
Lauya ya bukaci majalisar tarayya ta tsige shugaban kasa idan ba zai iya ba. Hoto: @Abbahikima, @officialABAT
Asali: Twitter

"Talaka ya koma cin tafasa" - Lauya Hikima

A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok, lauyan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Talaucin da mu ke ciki a Najeriya ba Allah ne ya kawo shi ba, mu muka kakabawa kanmu, domin Allah ya ba mu albarkatun kasa da ma'adanai.
""A Najeriya ne za ka ji an ce mutum daya ya saci kudin jama'a na biliyoyi da tiriliyoyin kudi, amma a lokacin ne za ka ga talaka na rasa abin da zai ci.
"Mu na gani yanzu yadda mutane suka koma cin tafasa domin su rayu, kuma an ba mu tabbacin cewa ba a kauye kadai ake haka ba, har a birni ma ana cin tafasar."

Kara karanta wannan

"Ba mu bukatar shikafarka": Malamin Musulunci ya nemi bukata 1 wurin Tinubu

Hikima ya yi magana kan zanga-zanga

Abba Hikima ya ce matasan Najeriya masu shirin yin zanga-zanga sun ba gwamnati dama domin duba halin da ake ciki, amma ba abin da ya faru.

Lauyan ya ce shi ba zai yi zanga-zanga da kowa ba, amma lallai matasa sun kai makurar da wa'azi ba zai yi tasiri a kansa ba, kuma hakurin 'yan kasar ya fara karewa.

A yayin da ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta samar da matakan magance yunwa, inganta rayuwar talaka, ya kuma ba majalisar tarayya shawarwari.

"A tsige shugaban kasa" - Hikima

Fitaccen matashin lauyan ya ce ma damar shugaban kasa ya gaza magance matsalolin da ke addabar kasar to ya kamata 'yan majalisar tarayya su taru su tsige shi.

"Idan har shugaban nan ba zai iya ba, sanatoci da 'yan majalisun tarayya su na da ikon yin zama su tsige shugaban domin doka ta basu wannan damar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Halin da matashin da ya yi hudubar jefo malamai daga mimbari yake ciki

"Kuma 'yan sandan da ke bi suna kama matasan da suke yin kira da ayi zanga-zanga, ba za ku iya ba, domin girman dakin ajiye masu laifuffukanku ya yi kadan ya dauki 'yan kasar."

- A cewar Abba Hikima.

Kalli bidiyon a kasa:

Yobe: Matasa sun yaga fastocin Tinubu

A yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga, a hannu daya kuma mun ruwaito cewa matasan Damaturu sun yanga manyan alluna dauke da hotunan Bola Tinubu.

A ranar Asabar ne Shugaba Tinubu ya ziyarci jihar Yobe inda ya kaddamar da wani shiri kan noma, sai dai bayan kaddamarwar matasan suka hau kan allunan suka lalata su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.