Zanga Zanga: Kungiyar Amnesty Intl ta Caccaki Gwamnati kan Kama 'Dan gwagwarmayan Tiktok

Zanga Zanga: Kungiyar Amnesty Intl ta Caccaki Gwamnati kan Kama 'Dan gwagwarmayan Tiktok

  • Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya (Amnesty International) ta ce gwamnatin tarayya ta karya doka bisa kama matashin dan tiktok
  • Jami'an tsaro sun tesa keyar matashin dan tiktok, Junaidu Abdulahi da aka fi sani da Abu Salma bisa kiran gudanar da zanga-zanga
  • Amnesty International ta shaida wa Legit cewa bai kamata gwamnati ta sa a kama shi ba ganin cewa matashin ya janye kalamansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar kare hakkin dan Adam da Amnesty International ta caccaki gwamnati bisa kama matashin dan tiktok, Junaidu Abdullahi saboda bayyana ra'ayinsa.

Kara karanta wannan

Shiga jami'a: Duk da dage kayyade shekarun dalibai, tsohon Sanata ya taso gwamnati a gaba

Amnesty International (AI) na ganin gwamnati ta yi riga malam masallaci wajen gaggawar gurfanar da Junaidu a gaban kotu da ma dage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa nan da mako uku.

Gwamnati
Amnesty International te nemi gwamnati ta saki matashin dan tiktok, Junaidu Abdullahi Hoto: AbuSalma39/Ajuri Ngelale
Asali: TikTok

Daily Trust ta tattaro cewa matashin wanda ke amfani da sunan Abusalma39 a shafin tiktok ya shiga hannun jami'an tsaro bayan ya yi kira ga matasa su yi gangamin zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnatin Najeriya ta yi kuskure" - AI

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin kasar nan ta tafka kuskure wajen kama matashin dan Tiktok, AbuSalma.

Shugaban kungiyar na Najeriya, Isa Sanusi ya tabbatar wa Legit cewa matashin bai yi laifin komai ba saboda ya fadi ra'ayinsa.

Isa Sanusi ya kara da cewa babu inda aka haramta wa dan Najeriya fitowa ya fadi ra'ayinsa a kan gwamnatin da ke mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi dalilin rokon mazauna Yobe su kauracewa zanga zanga

AI: "Gwamnatin ta gaggauta sakin AbuSalma"

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya ta shawarci gwamnatin tarayya ta gaggauta sakin matashin da ta kama saboda kira ga matasa su fito zanga-zanga.

Ya shawarci gwamnatin ta saki mai fafutukar, Junaidu Abdullahi cikin gaggawa, domin tuni ya janye kalamansa kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Tiktok.

Gwamnatin ta nemi a kaurace wa zanga-zanga

A wani labarin kuma kun ji yadda gwamnatin Yobe ta roki mazauna jihar da su kaurace wa zanga-zangar gama gari da wasu ke shirya wa a Najeriya saboda tsaronsu.

Gwamnatin ta fake da cewa jihar ba ta dade da farfado wa daga illar da matsalar ta'addancin Boko Haram ta jefa su a ciki ba., saboda haka shiga zanga-zanga zai kara kawo wata matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.