Fasinjoji sun Tsallake Rijiya da Baya Bayan Tayoyin Jirgin Sama Sun yi Bindiga a Adamawa

Fasinjoji sun Tsallake Rijiya da Baya Bayan Tayoyin Jirgin Sama Sun yi Bindiga a Adamawa

  • Allah ya kare afkuwar masifar hadarin jirgin sama a jihar Adamawa bayan fashewar tayoyin wani jirgin saman
  • Fasinjoji 199 a jirgin Max Air ne su ka tsira yayin da tayoyin jirgin guda shida su ka yi bindiga ana kokarin tashi
  • Yanzu dai an tabbatar babu ko mutum daga da ya samu rauni, kuma tuni hukumomi su ka fara binciken fashewar tayoyin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa - Fasinjoji 119 da masu aiki shida ne su ka tsira daga hadarin jirgi bayan tayoyin jirgin saman da su ke ciki ya yi bindiga a Adamawa.

Kara karanta wannan

Duk da dokar hana fita, 'yan bindiga sun kutsa kauye da dare, sun hallaka jama'a

Jirgin Max Air Boeing 737 na shirin tashi daga filin jirgin Yola a jihar Adamawa a yammacin Lahadi, inda a lokacin ne tayoyin su ka rika fashe wa.

Max Air
Tayoyin jirgi shida sun fashe a Adamawa Hoto: Max Air Ltd
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa daraktar hulda jama'a da kare hakkin abokan hulda, Bimbo Oladeji ta ce bayan an bayar da dama ga jirgin ya tashi ne aka ji kara, inda aka tabbatar da fashewar tayoyi guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Max Air: "Kowa na cikin koshin lafiya"

Kamfanin jirgin Max Air ya bayar da tabbacin cewa babu fasinja ko ma'aikata da su ka samu rauni a jihar Adamawa.

Wannan ya biyo bayan fashewar tayoyin jirginsa guda shida a kokarinsa na tashi daga Yola da ke Adamawa zuwa Abuja.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa daraktar hulda jama'a da kare hakkin abokan hulda, Bimbo Oladeji ta ce tayoyi biyu ne su ka fara fashe wa, kafin sauran su biyo baya.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi dalilin rokon mazauna Yobe su kauracewa zanga zanga

"Ana binciken" - Jirgin Kamfanin Max Air

Kamfanin Max Air ya ce ana gudanar da bincike domin gano musabbabin fashewar tayoyin jirginsa a filin jirgi na Yola.a.

Daraktar ta ce tuni cibiyar bincike ta Nigerian Safety Investigation Bureau ta isa filin jirgin.

Rundunar sojojin sama ta musanta hadarin jirgi

A baya mun ruwaito cewa rundunar sojojin saman Najeriya ta musanta cewa daya daga jiragenta masu saukar ungulu ya yi hadari a jihar Kaduna a safiyar Litinin.

Darakta kan harkokin yada labaran rundunar, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya ce wani jirgi mara matuki ne ya yi hadarin ba jirgi mara matuki ba kamar yadda ake fada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.