"Tana da Tausayi": 'Yan Gudun Hijira Sun Tura Bukata Ga Tinubu Kan Ministarsa
- 'Yan gudun hijira sun roki Shugaba Bola Tinubu ya tausaya musu wurin dawo da Ministar jin kai, Dakta Betta Edu
- 'Yan gudun hijirar da ke sansanoni a jihohin Borno da Niger sun yi rokon ne ganin yadda Edu ke tallafa musu
- Sun bukaci shugaban ya ji kansu wurin dawo da dakatacciyar Ministar kujerata domin ci gaba da ayyukan alheri da take yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - 'Yan gudun hijira a jihohin Borno da Niger sun roki Shugaba Bola Tinubu bukata ta musamman yayin da suke halin kunci.
Shugabannin sansanin gudun hijiran sun bukaci Tinubu ya dawo da dakatacciyar Ministar jin kai, Dakta Betta Edu.
'Yan gudun hijira sun roki Tinubu
Wannan na kunshe wata sanarwa da suka fitar mabambanta inda suka ce suna samun tallafi a lokacin tsohuwar Ministar, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suka ce cikin watanni hudu da rabi da Edu ta yi sun samu tallafi marar misaltuwa yayin ake tallafawa 'yan gudun hijira.
Usman Monguno wanda ke sansanin gudun hijira na Muna a Maiduguri da ke jihar Borno ya ce yana cikin sansanin fiye da shekaru shida.
Usman ya yabawa Shugaba Tinubu kan irin salon shugabancinsa musamman wurin tallafawa 'yan gudun hijira.
Ya roki Tinubu da ya taimaka ya dawo da Betta Edu inda ya ce ta himmatu wurin tallafa musu kamar yadda shugaban ke da muradi.
'Yan gudun hijira sun fadi amfanin Ministar Tinubu
A bangarensa, Abdullahi Ndako daga sansanin 'yan gudun hijira a jihar Niger ya ce ya shafe shekaru da dama a sansanin.
Ndako ya ce babbar kyauta da Tinubu zai yi musu ita ce dawo da Betta Edu domin ta ci gaba da aikin alheri da take yi.
Ya ce kwanaki kadan bayan nada ta mukami, Edu ta kawo ziyara inda ta zo da kayan tallafi tare da maganganu masu dadi.
'Yan gudun hijira sun cika sansani da jarirai
A wani labarin, kun ji cewa hukumomi sun fara korafi kan yadda 'yan gudun hijira suka cika sansaninsu da jarirai a jihar Benue.
Hukumomin sun nuna damuwa kan yadda ake haifan jarirai duk da rashin ingantaccen lafiya da abinci da ake fama da shi.
Asali: Legit.ng