Yadda Kirsita Ya Sadaukar da Rayuwarsa Domin Kula da Mahaifyar Rarara
- Awanni bayan kama wani da ake zargi da sace mahaifiyar Rarara, mawakin ya tura sakon godiya ga al'umma kan addu'o'insu
- Mawaki Rarara ya bayyana yadda wani Kirista ya sadaukar da rayuwarsa domin kula da mahaifiyarsa mai suna Hauwa Adamu
- Ya ce mutumin ya cika ka'idojin da maharan za su sake shi amma ya gwammace ya zauna domin ci gaba da kula da mama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya yi godiya ga wadanda suka taya su da addu'o'i bayan sace mahaifiyarsa.
Rarara ya ce ya sha mamaki bayan wani Kirista ya sadaukar da rayuwarsa a hannun 'yan bindiga domin kawai ya taimaki mahaifiyarsa.
Yadda Kirista ya kula da mahaifiyar Rarara
Mawakin ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Asabar 20 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rarara ya ce wani Kirista ne ya dauki nauyin kula da mahaifiyarsa mai suna Hauwa Adamu duk da cewa lokacin sakinsa ya yi.
Ya ce mutumin ya tausaya mata bayan ganinta tana kuka a ranar da ya samu 'yanci daga hannun miyagun amma ya zauna domin kula da ita.
Rarara ya godewa al'umma da addu'o'i
"Tabbas addu'oinku sun yi matukar tasiri wurin sako mama daga hannun 'yan bindiga, ina godiya matuka."
"Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne yadda wani Kirista ya zabi ci gaba da zama a hannun 'yan bindiga domin kula da mahaifiyata."
"An kama shi wata daya kafin zuwan mama inda ya ke shirin barin hannunsu bayan cika ka'aidoji amma ya ki tafiya saboda mama."
"Lokacin da ya ga mama tana kuka, ya sha alwashin zama har sai an saki mama inda ya kara makwanni biyu saboda kula da ita."
- Dauda Kahutu Rarara
Rarara ya ce abin mamaki shi ne wannan mutumin ba ya ma addini daya da mama tana sallolinta da addu'o'i shi ma yana na shi domin samun tsira daga miyagun.
An kama wadanda suka sace mahaifiyar Rarara
Kun ji cewa Hukumar DSS a jihar Kano ta kama wani da ake zargi da hannu a sace mahaifyar mawaki Dauda Kahutu Rarara.
Hukumar ta yi nasarar hallaka daya daga cikinsu inda ta yi nasarar samun makudan kudi har N26.5m daga hannun 'yan ta'addan.
Asali: Legit.ng