Kano: Bidiyon Yadda Dubban Jama'a Suka Tarbi Aminu Ado a Taron Saukar Akur’ani

Kano: Bidiyon Yadda Dubban Jama'a Suka Tarbi Aminu Ado a Taron Saukar Akur’ani

  • A yau Asabar 20 ga watan Yulin 2024 aka gayyaci Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero zuwa addu'a ta musamman da aka shirya
  • An gano Aminu Ado a cikin wani faifan bidiyo bayan ya isa wurin gudanar da addu'o'i da saukar Alkur'ani mai girma a Goron Dutse
  • Za a gudanar da addu'o'in ne a gidan marigayi Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu da yammacin yau Asabar 20 ga watan Yulin 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya amsa gayyatar da aka yi masa domin halartar saukar karatun Alkur'ani.

Aminu Ado ya amsa gayyatar a yau Asabar 20 ga watan Yulin 2024 a gidan Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu a Goron Dutse da ke Kano da yammaci.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi babban kamu a APC bayan sauya shekar mataimakin gwamna

Aminu Ado ya sauka gidan marigayi Isyaka Rabiu domin halartar taro
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado ya sauka gidan Isyaka Rabiu domin saukar Alkur'ani. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Dubban jama'a sun tarbi Aminu Ado

A cikin wani faifan bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a shafin X an gano isar Aminu Ado gidan marigayi Khalifa Isyaka Rabiu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gayyace shi ne domin gudanar da addu'a ta musamman ga kasa baki daya wanda Khalifa Sheikh Nafiu Muhd Isyaka Rabiu ya shirya.

An gano dandazon jama'a suna shewa da murna yayin da suke tarbar sarkin Kano na 15, Aminu Ado a gidan shehin domin gudanar na addu'o'in.

An gudanar zikiri a fadar Aminu Ado

Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zikirin Juma'a a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado wanda iyalan Shiekh Dahiru Bauchi suka shirya.

Iyalan sun shirya zikirin ne na musamman domin yin addu'o'i ga kasa duba da halin da ake ciki na tsadar rayuwa da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

"Sun yi barazanar kashe ni," Dan Bilki ya nace gwamna Uba Sani ne ya sa a zane shi

Daga cikin wadanda aka gayyata zikirin na musamman akwai Shugaba Bola Tinubu a matsayin babban bako a wurin taron.

Sanusi II ya koka kan halin kunci

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammdu Sanusi II ya nuna damuwa kan halin kunci da ake ciki a fadin kasar baki daya.

Sanusi II ya ce suna yawan samun korafe-korafe daga hakimai a fadin jihar kan irin mawuyacin hali da ake ciki na tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.