Gwamnoni Sun Shiga Rudani Kan Albashin N70,000, an Fadi Jihohin da Za Su Biya

Gwamnoni Sun Shiga Rudani Kan Albashin N70,000, an Fadi Jihohin da Za Su Biya

  • Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata bayan wata ganawa da kungiyar NLC
  • Gwamnonin wasu jihohi sun bayyana cewa sun shirya biyan mafi karancin albashi ga ma'aikatansu duba da halin da ake ciki
  • Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikaci a ma'aikatar lafiya da ke jihar Gombe kan mafi karancin albashin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnonin jihohi da dama a Najeriya sun shiga rudani kan mafi karancin albashin N70,000 da aka amince da shi.

Gwamnoni da dama sun ki cewa komai game da biyan mafi karancin albashin inda suke sauraran ganawar kungiyarsu ta NGF.

Wasu gwamnonin jihohi sun shirya biyan mafi karancin albashi
Gwamnoni da dama na jiran ganawa ta musamman kan mafi karancin albashin N70,000. Hoto: Nigeria Governors Forum.
Asali: Facebook

Wasu gwamnoni sun ki magana kan albashin

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Jerin gwamnonin da suka amince za su biya N70,000

Duk da haka wasu gwamnoni sun tabbatar da cewa za su iya biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashin, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu jihohi sun zabi tattaunawa kan lamarin kafin fitar da matsaya yayin da wasu ke jiran sanarwa daga takwarorinsu.

Gwamnatin jihar Osun ta tabbatar da shirinta na fara biyan mafi karancin albashin ga ma'aikata ba tare da matsala ba, Leadership ta tattaro.

Gwamnonin da suka amince da biyan albashin

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce a shirye ya ke ya biya albashin idan har sauran jihohi sun aminta da karin albashin.

Har ila yau, Gwamnan jihar Benue, Alia Hyacinth ya ce shi ma ya shirya biyan mafi karancin albashin da za rar ta tabbata.

Jihar Akwa Ibom da Nassarawa sun bi sahun sauran jihohi da suka shirya biyan albashin ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Malami ya kasafta yadda karamin ma’aikaci zai karar da albashin N70, 000 a abinci a wata

Sauran jihohi kamar Kwara da Adamawa ba su bayyana matsaya ba kan sabon albashin duk da amincewa da NLC ta yi.

Jihohi kamar Kano da Rivers da Ebonyi da Abia da sauran jihohi suna ci gaba da tattaunawa da kuma jiran ganawar kungiyar gwamnonin Najeriya.

Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikaci a ma'aikatar lafiya da ke jihar Gombe kan mafi karancin albashi.

Muhammad Aliyu ya ce har yanzu dai suna jiran martanin gwamnan Gombe game da biyan albashin N70,000 din.

"Wasu gwamnonin jihohi da dama sun ba da tabbacin biyan albashin da za ran an tabbatar da hakan."
"Duk da haka muna rokon mai girma gwamna ya duba halin kunci da ake cikin domin amincewa da sabon albashin."

- Muhammad Aliyu

NLC ta amince da N70,000 daga Tinubu

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan Najeriya.

Kungiyar kwadago ta NLC tuni ta amince da sabon mafi karancin albashin tare da yabawa shugaban kan irin wannan kokari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.