Zargin Biyan Malamai N16m Domin Rufe Masu Baki Ya Fusata Sheikh Mansur Sokoto

Zargin Biyan Malamai N16m Domin Rufe Masu Baki Ya Fusata Sheikh Mansur Sokoto

  • Mansur Ibrahim Sokoto ya yi kaca-kaca da wadanda su ke jifan malamai da zargin karbar kudi a hannun gwamnati
  • Babban malamin ya soki masu taba malaman musulunci, ya karyata cewa sun karbi N16m domin rufewa jama’a baki
  • Sheikh Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya ce malamai sun dage wajen ankarar da gwamnatin Bola Tinubu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Malamai magada Annabawa ne wadanda mutanen kwarai su ke ganin kima, martaba da kuma darajarsu a cikin al’ummar musulmi.

A ‘yan kwanakin nan, halin matsin rayuwa da aka shiga ya kai wasu sun zame, su na cin mutuncin malamai saboda sun kushe zanga-zanga.

Mansur Sokoto
Sheikh Mansur Sokoto ya ji haushin masu bata malamai Hoto: Prof. Mansur Sokoto, mni
Asali: Facebook

An ji a Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto wanda babban malami ne da ake ji da shi a duniyar ilmi ya na maidawa mutane martani a dandalin X.

Kara karanta wannan

"Ba mu bukatar shikafarka": Malamin Musulunci ya nemi bukata 1 wurin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mansur Sokoto ya fusata da zargin N16m

Bidiyon malamin yana dauke da fusataccen martini ga wadanda su ke zargin gwamnati ta biya N16m, ta saye malaman addini a Najeriya.

Kamar yadda aka ji a bidiyon da wani Mu’amar Gaddafi ya daura, Mansur Ibrahim Sokoto ya yi kaca-kaca da masu neman bata malaman addini.

Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto ya nuna ko a kan N16tr ba zai sayar da al’ummarsa ba, balle masu yada jita-jitar cewa sun karbi miliyoyi.

Sheikh Mansur Sokoto a kan malaman kwarai

Malamin ya hakaito zancen da wani ya yi da ya ji wasu marasa kunya su na ikirarin cewa a halin yanzu malaman Allah SWT sun kare a kasar.

Shehin ya ce duk mai ganin malaman kwarai sun kare, sai ya daura ubansa a kan mimbari.

Farfesan wanda malamin ilmin musulunci ne a jami’ar Danfodio da ke jihar Sokoto ya yi bayanin yadda suke ta fadawa gwamnati gaskiya.

Kara karanta wannan

Shin da gaske an aikawa malamai N16m domin hana matasa zanga-zanga a Arewa?

A cewar masanin hadisin, malamai 130 su ka tare a birnin Abuja domin su ankarar da gwamnatin Bola Tinubu kan halin da ake ciki a yau.

Ana haka kuma sai wasu su ka rika yawo da labari cewa an biya malamai kudi domin su hana matasan yankin Arewa shirya zanga-zanga.

Daga baya malamin ya janye kalamansa, ya bayyana cewa ya yi magangunn ne a cikin fushi, kuma ya nemi a goge bangaren a cikin karatun nasa.

Sheikh Rijiyar Lemu ya yi kira

A kwanakin baya aka samu labari cewa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi nasiha ta musamman a kan masu rike da madafan iko a Najeriya.

Shehin malamin ya ce dole ne a hukunta mai laifi idan ana so zaman lafiya da kwanciyar hankali ya daure ganin yadda ake sakin masu aika-aika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng