MNJTF: Dakarun Sojoji Sun Fadi Adadin ’Yan Boko Haram da Suka Tuba a Cikin Mako 1 Kacal

MNJTF: Dakarun Sojoji Sun Fadi Adadin ’Yan Boko Haram da Suka Tuba a Cikin Mako 1 Kacal

  • Dakarun sojin haɗin guiwa, MNJTF ta bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram 263 ne suka miƙa wuya tare da tuba a Kamaru
  • Kamar yadda shugaban fannin yaɗa labarai na MNJTF, Abubakar Abdullahi ya bayyana, dukkanin tubabbun 'yan Najeriya ne
  • Ya sanar da yadda mata, manyan maza da ƙananan yara suka fito daga maboyarsu tare da miƙa wuya ga dakarun rundunar

Kamaru - Aƙalla 'yan Boko Haram 263 ne tare da iyalansu suka miƙa wuya ga rukuni na daya na dakarun sojin haɗin guiwa (MNJTF) a Kamaru.

Wannan na ƙunshe ne a wata wasika da Abubakar Abdullahi, shugaban fannin yaɗa labarai na sojojin MNJTF ɗin dake N'djamena, Chadi.

Rundunar tsaron hadin guiwa ta MNJTF ta yi magana kan 'yan Boko Haram da suka mika wuya
Rundunar MNJTF ta ce 'yan Boko Haram 263 suka mika wuya a cikin mako 1. Hoto: @MNJTFOfficial
Asali: Twitter

Abubakar Abdullahi ya ce 'yan ta'addan sun miƙa wuya tsakanin 11 ga Yuli da 17 ga Yuli, yayin atisayen Lake Sanity II da ake yi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya zama na farko a Arewa da ya amince zai fara biyan ma'aikata N70,000

MNJTF ta karbi tubabbun 'yan Boko Haram

Daga cikin wadanda suka mika wuta akwai wani Malum Kori Bukar, mai shekaru 50 da ya tsere daga maboyarsu a Jibilaram tare da mika wuya ga dakarun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Guguwar miƙa wuyan ta fara ne a ranar 1 ga Yuli, yayin da 'yan ta'adda suka mika wuya ga dakarun MNJTF a Wulgo, a kan iyakar Kamaru."
“Binciken farko ya nuna cewa waɗannan mutanen sun fito daga Tumbuma da Kutumgulla a karamar hukumar Marte ta Najeriya."

'Yan Boko Haram 263 sun mika wuya

Sanarwar dakarun sojin MNJTF ta ci gaba da cewa:

"Bugu da ƙari, a ranar 11 ga Yuli, 'yan ta'adda 19 sun miƙa wuya a ƙauyen Madaya, can Arewacin Kamaru, da wasu 11 da suka miƙa wuya a Wulgo daga maboyarsu a Tumbuna.
“A ranar 12 ga Yulin 2024, wasu mutum 64 sun miƙa wuya a Bonderi dake Kamaru. An samu karin wasu 'yan ta'addan 27 da suka miƙa wuya a ranar 13 ga Yuli."

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa ƴan ƙwadago alƙawari 1 bayan amincewa da albashin N70,000 a Aso Villa

Rahoton Channels TV ya bayyana cewa, Abdullahi mai muƙamin Laftana Kanar, ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa waɗanda suka miƙa wuyan 'yan Najeriya ne.

'Yan bindiga sun kai hari Zamfara

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa miyagun 'yan ta'adda sun kai farmaki garin Dan Isah dake karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara.

An gano cewa, sun yi garkuwa da mutane 150 yayin da suka halaka wasu mutane biyar, mummunan harin da al'ummar yankin ba su taba ganin irinsa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.