Zanga Zanga: Malamin Musulunci Ya Yi Addu'ar Kawo Karshen Mulkin Tinubu, Ya Yi Tone Tone
- Malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Murtala Bello Asada ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu da masu kushe zanga-zanga
- Sheikh Asada ya ce ko kadan ba zai taba yin shiru kan abubuwan da suke faruwa ba musamman rashin tsaro a yankin Arewa
- Malamin ya roki Allah ya sa zanga-zanga ta kawo karshen mulkin Tinubu ko kuma a yi juyin mulki a kasar saboda ya fi alheri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Fitaccen malamin Musulunci, Malam Murtala Bello Asada ya magantu kan shirin zanga-zanga da ake yi.
Malamin ya ce mutane su na cikin mawuyacin hali musamman a Zamfara da Sokoto da Katsina fiye da matsalar zanga-zanga.
Zanga-zanga: Murtala Asada ya soki mulkin Tinubu
Murtala Bello Asada ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da @deedatAhmadd a shafin X inda ya ce suna rokon Allah ya kawo zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce mutanen Arewa su na cikin masifar da ta fi karfin zanga-zanga da ake ta ihu a kai inda ya roki Allah ya kawo mulkin soja.
"Ana zanga-zanga za ta jefa kasa cikin hatsari, wanda ke rayuwa a Zamfara da Sokoto da Katsina ji yake ba da shi ake ba."
"Daman su sun saba da masifar ana zuwa a kama mutane yafi 50 ko 100 a kauyensu, yanzu kididdiga ta nuna akwai dubban mutane hannun 'yan ta'adda."
- Murtala Asada
Murtala Asada ya yi addu'ar juyin mulki
"Mutane da yawa idan aka sako su ba su da amfani ka ce wai zanga-zanga zai jawo fitina? Muna rokon Allah ya sa zanga-zanga ta kawo karshen mulkin Bola Tinubu."
"Muna rokon Allah ya kawo juyin mulki a Najeriya in yaso gobe a bude kasa ta bakwai a jefa Murtala Bello."
- Murtala Bello Asada
Malamin ya sha alwashin ba zai taba barin wadannan maganganu ba ko mene zai faru da shi sai dai ya faru.
Daurawa ya tsorata da mulkin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da mulki a gwamnatin Bola Tinubu.
Daurawa ya ce abubuwan da suke faruwa a gwamnatin sun fara ba shi tsoro yadda ake dakatarwa ko korar masu fadan gaskiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng