Gwamnati Ta Fadi Ainihin Halin da Matatar Dangote Take Ciki, Ashe Ba Ayi Rabin Aiki ba

Gwamnati Ta Fadi Ainihin Halin da Matatar Dangote Take Ciki, Ashe Ba Ayi Rabin Aiki ba

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin shigo da man fetur daga ƙasashen ketare duk da cewa matatar man Dangote ta fara aiki
  • Shugaban hukumar lura da man fetur ta kasa, Farouk Ahmed ne ya bayyana haka a birnin Fatakwal a jiya Alhamis, 18 ga watan Yuli
  • Haka zalika Farouk Ahmed ya bayyana matakin da matatar man Dangote da ke garin Legas ke ciki a hukumance a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Shugaban hukumar kula da man fetur ta kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed ya bayyana dalilin kin ba matatar man Dangote lasisi.

Farouk Ahmed ya kuma bayyana dalilin kin yarda da bukatar kamfanin Dangote ta hana wasu shigo da kayan da suka shafi danyen mai daga waje.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba JAMB sabon umarni kan adadin shekarun shiga jami'o'i da makarantu

Matatar Dangote
Gwamnati ta yi magana kan rashin sayen mai a matatar Dangote. Hoto: Dangote Foundation
Asali: Facebook

Jaridar the Cable ta ruwaito cewa shugaban hukumar NMDPRA ya bayyana haka ne yayin wani taro a jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin matatar man Dangote a hukumance

Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed ya bayyana cewa a yanzu haka matatar man Dangote da ke Legas ba ta wuce kashi 45% wajen kammaluwa ba.

Saboda haka ne ma Farouk Ahmed ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta ba Dangote lasisin matatar ba.

NMDPRA: 'Ba mu adawa da Dangote'

Farouk Ahmed ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta adawa da cigaban Aliko Dangote kamar yadda wasu ke yaɗawa, rahoton Premium Times.

Shugaban NMDPRA ya ce ana ga kamar suna adawa da Dangote ne lura da yadda suke sayen man fetur daga waje amma suna da dalili.

Ya ce a yanzu haka matatar man Dangote tana matakin gwaji ne kuma ba za ta iya watadar da Najeriya ba.

Kara karanta wannan

"Tinubu na kokari, kar ku shiga zanga zanga," Minista ya lallabi jama'a

An yarda kowa ya shigo da mai

Farouk Ahmed ya bayyana cewa kamfanin Dangote ya bukaci gwamnatin tarayya ta saka masu sayen abubuwan da suka shafi nan fetur su rika saye a wajensa.

Amma gwamnatin ta barsu su rika saye daga waje saboda har yanzu matatar man Dangote ba ta gama kammaluwa ba.

Rage farashi: Matatar Dangote ta yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa matatar man Aliko Dangote ta ƙaryata rade-radin cewa ta rage farashin dizal ne saboda rashin ingancin kayanta.

Kamfanin ya yi wannan martanin ne yayin da mutane da dama yaɗa jita-jitar cewa man da take samarwa ba shi da inganci sosai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng