Bayani Dalla Dalla: Yadda Za Ku Binciki Kudin da Kananan Hukumominku Ke Samu Duk Wata

Bayani Dalla Dalla: Yadda Za Ku Binciki Kudin da Kananan Hukumominku Ke Samu Duk Wata

  • An samu cikakken bayani kan yadda ake duba kudin da gwamnatin tarayya ke aikewa kowace karamar hukuma a Najeriya
  • Wannan ci gaban na zuwa ne bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke na bai wa kananan hukumomi yancin kula da kudinsu
  • Kotun koli ta kuma dakatar da gwamnonin daga rusa zababbun ciyamomin kananan hukumomi da kuma nada kantomomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke na bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu, Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin bayyanawa kowa kudin da ake turawa kananan hukumomin.

A martanin da ya mayar kan hukuncin, Shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika yi wa kananan hukumominsu hisabi kan kudin da suke karba daga tarayya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: NLC ta yi barazanar tsunduma wani yajin aiki, an gano dalili

Shugaba Tinubu ya sha alwashin bayyanawa jama'a kudin da ake turawa kananan hukumomi
Bayani dalla dalla na yadda za ku duba kudin da ake turawa kananan hukumominku a wata. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A wani sabon ci gaba, shafin BudgiT ya bayyana jerin matakai ga ’yan Najeriya domin sanin abin da ake aika wa kananan hukumominsu a daga asusun tarayya na FAAC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakan duba kudin kananan hukumomi

A nan ƙasa, akwai jerin mataki-mataki na duba kudin da gwamnatin tarayya ke aikawa ƙananan hukumominku a kowanne wata:

  1. Rubuta me.budgit.org a manhajar shiga yanar gizonka
  2. Ka fara yin sabuwar rijista da shafin.
  3. Ka shigar da sunanka, jiharka, da karamar hukumarka.
  4. Nan take za ka ga bayanan kudin da jiha da karamar hukumarka ke samu.

Kotu ta ba kananan hukumomi 'yanci

Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli ne muka ruwaito cewa Kotun Koli ta bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu na kudi a Najeriya.

Kotun Kolin ta kuma gwamnatin tarayya ikon rike kudin duk wata karamar hukuma da ba a gudanar da zaben shugabanninta ba.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tinubu ya fadi sabon mafi karancin albashi tare da daukar alkawura 3

Kotun kolin ta kuma jaddada cewa ya saba ka'ida yadda gwamnonin ke tafiyar da al’amuran kananan hukumomi ta hanyar nada kantomi, inda ta hana su rusa ciyamomin da aka zaba.

Za a kirkiri hukumar zaben kananan hukumomi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanatan Neja ta Gabas, Sani Musa ya gabatar da wani kuduri gaban majalisar dattawa, na kirkirar hukumar zaben kananan hukumomi.

Idan kudirin ya tabbata, hukumar za ta kasance daya tilo da za ta rika gudanar da zabukan kananan hukumomi a fadin kasar wanda zai kara rage ikon gwamnoni kan ciyamomi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.