Kudin kananan hukumomi: Gwamnoni sun bukaci ya tsawatar wa NFIU a kan sa musu ido
Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsawatar wa da hukumar nan dake binciken harkokin kudi a sirrance (NFIU) a kan sa ido dangane da kudaden da ake bawa kananan hukumomin kasar nan.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Abdulrazaque Bello-Barkindo, shugaban sashen sadar wa da yada labarai a hedikwatar kungiyar gwamnoni (NGF), ya fitar a ranar Litinin.
Gwamnonin sun ce hukumar NFIU na yin shishigi wajen shiga harkokin da suka fi karfin ikon ta.
A takardar mai dauke da sa hannun Abdulaziz Yari, shugaban kungiyar NGF, gwamnonin sun yi Alla-wadai da abinda suka kira yunkurin bata suna da kimar su da hukumar NFIU ke yi.
A cikin makon jiya ne hukumar NFIU ta koka a kan yadda gwamnonin jihohi ke fitar da makudan biliyoyi daga asusun hadin gwuiwa da kananan hukumomi ba tare da bin ka'ida ba. Hukumar ta bayyana cewar wani gwamna ya fitar da fiye da biliyan N100 daga asusun tare da fadin cewar ya kamata a yi dokar da zata kawo karshen tabargazar da gwamnonin ke yi da kudaden kananan hukumomi.
Sai dai, gwamnoni sun bayyana matakin na NFIU a matsayin yin karen tsaye ga kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 1999.
Tuni hukumar NFIU ta sanar da hukumar EFCC tare da tsayar da ranar 1 ga watan Yuni domin fara aika wa kananan hukumomi kudin su kai tsaye.
DUBA WANNAN: Tabbas muna binciken Okorocha da wasu da dama - Magu
Amma gwamnonin, a cikin wasikar da suka fitar mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Mayu, sun yi watsi da wannan shawarar da NFIU ta yanke.
Yari ya jawo hankalin shugaban kasa a kan sashe na (6) (a) da (b) da ya bawa majalisun dokokin jihohi ikon yin doka a kan yadda jiha za tayi amfani da kudin kananan hukumomi a cikin jihohin su.
Ya bayyana cewar sashe na 162 (6) ya yi bayani a kan kirkirar asusun hadin gwuiwa tsakanin jiha da kanana hukuminta (SJLGA) wanda kuma a cikinsa ne tarayya zata ke aiko kudin jihar da kananan hukumomi duk wata.
Gwamnan ya jaddada cewar babu inda hukumar NFIU keda hurumin daukan matakin da ta dauka.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng