Ana Wata Ga Wata: NLC Ta Yi Barazanar Tsunduma Wani Yajin Aiki, an Gano Dalili

Ana Wata Ga Wata: NLC Ta Yi Barazanar Tsunduma Wani Yajin Aiki, an Gano Dalili

  • Kungiyar NLC karkashin Joe Ajaero ta bayyana damuwarta kan rashin biyan albashin wasu daga cikin mambobinta a bangaren ilimi
  • Bayan warware takaddamar mafi karancin albashi a ranar Alhamis, kungiyar kwadago ta lashi takobin shiga yajin aikin gama gari
  • Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan sanda suka hana kungiyoyin SSANU da NASU, daga gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Alhamis ne kungiyar kwadago ta NLC ta gargadi ga gwamnatin tarayya kan rike albashin watanni hudu na mambobin kungiyoyin ma'aikatan jami'o'in NASU da SSANU.

Kungiyar a cikin wata sanarwa da shugabanta mai kula da harkokin jama'a, Benson Upah ya fitar, ta ce gwamnati ta shirya ganin zanga-zangar a fadin kasar idan har ta ki biyan albashin.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tinubu ya fadi sabon mafi karancin albashi tare da daukar alkawura 3

NLC ta yi magana kan rike albashin ma'aikatan jami'o'i da gwamnati ta yi
NLC ta yi barazanar tsunduma yajin aiki saboda an rike albashin ma'aikatan jami'o'i. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Facebook

'Yan sanda sun hana zanga-zanga

Kungiyar ta NLC ta kuma caccaki kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Bennet Igweh, bisa zargin cin zarafin ma’aikatan jami’o'in da suka yi inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya dai mun rahoto cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dakatar da kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin SSANU da NASU daga gudanar da zanga-zanga a Abuja.

Hakan ya faru ne bayan shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya koka da cewa babu daya daga cikin yarjejeniyoyin da aka cimma da gwamnatin tarayya da aka aiwatar.

Dalilin NLC na shirin shiga yajin aiki

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa saboda abin da 'yan sandan suka yi wa mambobin kungiyoyin ma'aikatan jami'o'in, kungiyar NLC ta ce:

"Dalilin zanga-zangar lumana da NASU da SSANU suka yi abu ne a bayyane, shi ne hana su albashin da gwamnati ta yi na watanni hudu bayan an biya ma’aikata a wasu kungiyoyin.

Kara karanta wannan

Bayan hana ma'aikata albashin watanni 4, jami'an tsaro sun hana su zanga zanga

"Kungiyoyin biyu sun ƙare duk wata hanya ta neman hakkinsu bisa doka ciki har da yajin aikin gargadi amma ba a biya su ba, karshe kuma 'yan sanda suka dakile zanga-zangarsu.
"Muna gargadin gwamnatin tarayya da ta sani cewa babu abin da zai hanamu shiga yajin aikin gama gari ma damar aka ki biyan mambobinmu a NASU da SSANU bashin albashinsu."

Tinubu ya fadi mafi karancin albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya ayyana N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.

Sannan kuma shugaban kasar ya sha alwashin yin amfani da karfin ikonsa na warware albashin watanni hudu da gwamnati ta rike wa ma'aikatan jami’o’i.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.