Gaskiya Ta Fito: Sai da Tinubu Ya Yi wa Ƴan Ƙwadago Tayin N250,000 Amma Suka Ƙi Yarda
- Shugabannin kwadago sun ki amincewa da tayin Shugaba Bola Tinubu na biyan ₦250,000 matsayin mafi karancin albashi a Najeriya
- Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce 'yan kwadagon sun ki amincewa da wannan tayin saboda yana dauke da sharadi karin kudin mai
- Ajaero ya ce an gabatar da tayin ne a ganawar da suka yi da Shugaba Tinubu, kuma sun yi watsi da hakan ne domin amfanin ‘yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yi watsi da tayin Shugaba Bola Tinubu na biyan N250,000 matsayin mafi karancin albashi bisa sharadin kara farashin man fetur.
A cewar shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, Shugaba Tinubu ya gabatar da tayin ne a wata ganawa da ya yi da 'yan kwadagon a gidan gwamnati da ke Abuja a ranar Alhamis.
Ajaero ya bayyana cewa kungiyar kwadago ta ki amincewa da wannan tayin, inda ta zabi fifita jin dadin ‘yan Najeriya, kamar yadda rahoton Tribune ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabon albashi: NLC ta amince da ₦ 70,000
Yayin da yake magana da talabijin Channels, Ajaero ya ce sun amince da mafi karancin albashi na ₦70,000 domin gujewa 'yan Najeriya fadawa cikin wahala.
NLC ta jaddada cewa a shirye take ta sadaukar da muradunta, ma damar hakan zai kawo sauki ga ma'aikata da ma daukacin 'yan Najeriya.
An ce 'yan kwadago da gwamnatin tarayya sun sa hannu kan wannan matsayar da aka cimmawa, wadda ta tabbatar da karin sama da kashi 100 na mafi karancin albashin.
Tinubu zai aika sabon albashi ga majalisa
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai aika da kudirin dokar zartaswa ga majalisar tarayya domin yin bitar mafi karancin albashin da aka amince da shi, wanda daga nan ne zai zama doka.
Wannan ci gaban yana da nufin samar da sabon tsari mai dorewa na waiwayar dokar mafi karancin albashin a duk bayan shekaru uku.
Tinubu ya fadi sabon mafi karancin albashi
Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya ayyana N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.
Shugaba Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da hanyoyin da za su taimaka wa kamfanoni da kananan hukumomi wajen biyan mafi karancin albashin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng