Dan Gwamnan Borno Ya Kashe Ɗan China a Gidan Rawa? Umar Zulum Ya Yi Bayani a Bidiyo

Dan Gwamnan Borno Ya Kashe Ɗan China a Gidan Rawa? Umar Zulum Ya Yi Bayani a Bidiyo

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya musanta labarin dake yawo na cewa ɗansa Umar ya kashe wani ɗan China a gidan rawa
  • Shi ma Umar Babagana, ya fito a bidiyo ya karyata wannan jita-jita da ake yadawa, inda ya ce tsawon watanni yana Borno ba wai Indiya ba
  • Umar Babagana Zulum ya yi ikirarin cewa ana yada jita-jitar ne kawai domin a gogawa mahaifinsa, gwamnan Borno kashin kaji

Maiduguri, Borno - Umar Babagana Umara Zulum, dan gwamna Borno, ya musanta zargin cewa yana hannun hukuma bayan da ya kashe wani ɗan China a gidan rawa.

Idan ba a manta ba, akwai wasu jaridun yanar gizo da suka ruwaito cewa dan gwamnan ya kashe dan China a gidan rawa a Indiya saboda sun samu sabani akan wata budurwa.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya ba da umarnin a zane Dan Bilki Kwamanda? Gwamnatin Kaduna ta magantu

Dan gwamnan Borno ya karyata jita-jitar ya kashe wani dan China
Dan Gwamna Bababagana Zulum ya karyata rahoton cewa ya kashe dan China a Indiya. Hoto: @muhdzulum
Asali: Twitter

"Dan gwamna bai aikata laifi ba" - Bundi

Kamar yadda muka ruwaito, gwamnatin Borno ta ce Gwamna Zulum ba zai yi ƙasa a guiwa ba wurin daukar matakin shari'a kan masu shirya rahoton.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin gwamnan ya ce:

Gwamnan ba zai ƙasa a guiwa ba wurin ɗauka matakin shari'a kan duk wata jarida da ta cigaba da yaɗa labarin bogin nan kan dandalinta ba.
"Muna son sanar da jama'a cewa, babu ɗan Gwamna Zulum da aka kama ko ake tuhumarsa da aikata wani laifi, ko yake da hannu wurin aikata abinda ya saɓa shari'a a ko ina."

"Ban kashe kowa ba" - Dan Gwamna Zulum

A wani faifan bidiyo da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X, Umara Babagana Zulum, dan gwamnan Borno ya ce sam bai kashe kowa ba, sabanin rahoton da ake yadawa.

Kara karanta wannan

UTME: Jerin sunaye da jihohin ɗaliban da suka yiwa jarabawar JAMB cin kaca a 2024

"Ya ku 'yan Najeriya. Sunana Umara Babagana Umara Zulum, na zo nan domin jawabi game da ƙaryar da ake yaɗawa a kaina.
"Na samu labari cewa wai ana zargin na kashe wani a gidan rawa. Wannan ba gaskiya bane. Suna son ɓata sunan mahaifina ne. Ina tare da dangina tun wata biyu da suka wuce, ina Maiduguri."

- A cewar Umar Babagana Zulum.

Zulum zai tallafawa manoman Borno

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno zai gwangwaje manoma da takin zamani domin taimaka musu.

An samu wannan sanarwar a wata takardar da gwamnan ya fitar ta bakin mataimakin gwamnan, Umar Usman Kadafur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.