Ndume: Maganar Sheikh Daurawa Kan Matsawa Talaka a Mulkin Tinubu Ta Tada Ƙura
- Babban malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana kan tsige Sanata Ali Ndume
- Majalisar dattawan Najeriya ta tsige Sanata Ali Ndume ne biyo bayan kalaman da ya yi a kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Sai dai maganar da Aminu Ibrahim Daurawa ya yi ta tayar da kura a Arewa inda al'umma suka rika tofa albarkacin bakinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana kan yadda majalisar dattawa ta tsige Sanata Ali Ndume.
Hira ta zama sabuwa a dandalin sada zumunta a Arewacin Najeriya kan maganar da Sheikh Daurawa ya yi.
Legit ta bibiyi yadda al'umma suka yi martani kan kalaman da Sheikh Daurawa ya yi da abin da suka fada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsige Ndume: Martani kan kalaman Daurawa
Ameenu: 'Za mu yi zanga zanga'
Wani matashi mai suna Ameenu Isah a wallafa a karkashin rubutun da malam Daurawa ya yi Facebook cewa irin haka ne yasa suke son fita zanga zanga.
Ameenu Isah ya ce dole matasa su fita zanga zanga domin kwato ƴancinsu daga hannun shugabanni.
Mansur: 'Talaka ya koma ga Allah'
Wani mai amfani da kafar Facebook, Mansur Ahmed ya wallafa a karkashin rubutun Sheikh Daurawa cewa ba abin da ya saura ga talaka a Najeriya sai bin Allah.
Mansur ya ce a yanzu shugabanni ba su duba halin da talakawa ke ciki ko sun nuna sun damu ma kawai da baki ne.
Saad: 'Kun ce a cigaba da addu'a'
Kwamared Saad Sani Gombe ya bayyana cewa irin haka ne ya sanya talakawa yin korafi amma malamiai suka rika cewa a cigaba da addu'a.
Saad ya kara da cewa dole a tashi a nemi mafita a Najeriya domin Musulunci bai yarda mutum ya zauna a rika cutar shi ba.
Yan Hisbah sun ziyarci Sanusi II
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin Hisbah a kananan hukumomi 44 a Kano sun yi mubaya'a ga Sarki Muhammadu Sanusi II a jihar.
Kwamandojin sun ziyarci sarkin ne a fadarsa domin nuna goyon bayansu bayan dawowarsa kan karaga karkashin jagorancin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Asali: Legit.ng