Ministan Tinubu Ya Gamu da Matsala Bayan Kayyade Shekarun Shiga Manyan Makarantu

Ministan Tinubu Ya Gamu da Matsala Bayan Kayyade Shekarun Shiga Manyan Makarantu

  • Masu ruwa da tsaki a harkar manyan makarantun Najeriya sun yi wa ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman bore a wani taron tsare-tsare
  • A yayin taron ne, Farfesa Mamman ya shaidawa masu ruwa da tsakin cewa an kayyade shekarun shiga manyan makarantu zuwa 18 ga dalibai
  • Sai dai ganin yadda masu ruwa da tsakin suka ki amincewa da wannan ka'ida ya tilastawa ministan rage shekarun shiga makarantun zuwa 16

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya yi watsi da umarnin da ya bayar da kayyade shekara 18 a matsayin adadin shekarun shiga manyan makarantu.

A wani taron tsare-tsare da hukumar JAMB ta shirya a Abuja, Farfesa Mamman ya bayyana cewa wadanda suka kai shekaru 18 zuwa sama ne kawai suka cancanci shiga manyan makarantun.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba JAMB sabon umarni kan adadin shekarun shiga jami'o'i da makarantu

Ministan Ilimi ya yi magana kan kayyade shekarun shiga manyan makarantu
Ministan Tinubu ya soke shekara 18 matsayin shekarun shiga manyan makarantu. Hoto: @ProfTahirMamman
Asali: Facebook

Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kalaman ministan ya haifar da ce-ce-ku-ce a yayin da masu ruwa da tsaki a manyan makarantun kasar suka yi adawa da adadin shekarun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Tinubu ya gamu da bore

Zauren taron ya kaure da hayaniya a lokacin da Farfesa Mamman ya sanar da adadin shekarun da gwamnati ta kayyade na shiga manyan makarantun.

A wani yunƙuri na kwantar da tarzomar, ministan ya yi tambaya, “muna tare?”, inda mahalarta taron suka yi amsa kuwwa da cewa “Ba mu tare."

Rahotanni sun bayyana cewa har sai da magatakardan hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya shiga tsakani, kafin jama'ar wajen suka kwantar da hankulansu, jaridar Vanguard ta ruwaito.

An rage shekarun shiga manyan makarantu

Yayin da yake mayar da martani game da korafin da mahalarta taron suka yi, ya dage cewa doka ce ta bukaci ‘ya’yansu su shiga manyan makarantu suna da shekara 18, bayan sun yi makarantar firamare da sakandare na shekaru 12.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun buɗe wuta kan matafiya, sun yi awon gaba da mutane da yawa

Ministan ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin tabbatar da cewa tsarin shigar da dalibai manyan makarantu na shekarar 2024/2024 ya yi daidai da tsarin doka.

Amma daga baya ministan ya amince da shawarwarin masu ruwa da tsaki na cewa daga shekaru 16 zuwa sama ya kamata dalibai su cancanci shiga manyan makarantun.

Gwamnati ta ba hukumar JAMB umarni

Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwa kan adadin shekarun da ake bukata kafin shiga manyan makarantu.

Gwamnatin ta ba hukumar kula da jarabawa ta JAMB umarnin cewa ta tabbatar sai masu shekaru 18 za a ba gurbin karatu a Jami'o'i da manyan makarantu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.