Babban Hafsan Tsaro Ya Ba Kwamandoji Umarni Ana Shirin Fara Zanga Zanga

Babban Hafsan Tsaro Ya Ba Kwamandoji Umarni Ana Shirin Fara Zanga Zanga

  • Christopher Musa ya umarci kwamandojin hukumomin tsaro da ke yaƙi da satar man fetur a yankin Neja Delta su kawo ƙarshen matsalar
  • Babban hafsan tsaron na Najeriya ya ba su wa'adin makonni biyu su murƙushe ɓarayin man fetur
  • Lafatanar Janar Christopher Musa ya bayyana cewa duk jami'in tsaron da aka kama na haɗa baki da ɓarayin zai fuskanci hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Babban hafsan tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa, ya ba da umarni ga kwamandojin hukumomin tsaro da ke yaƙi da satar man fetur a yankin Neja Delta.

Janar Christopher Musa ya umarce su da su kawo ƙarshen satar man fetur a yankin nan da makonni biyu.

Kara karanta wannan

Jira ya ƙare, Shugaba Tinubu zai sanar da adadin sabon mafi ƙarancin allbashi a Najeriya

Babban hafsan tsaro ya umarci a kawo karshen satar man fetur a Neja Delta
Babban hafsan tsaro ya ba kwamandoji wa'adin mako biyu kan satar man fetur Hoto: @DefenceInfo
Asali: Facebook

Baban hafsan tsaron ya bada wannan umarnin ne yayin ganawa da shugabannin tsaro na Operation Delta Safe a yankin Neja Delta a Port Harcourt ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya damu kan ayyukan ɓarayin mai

Janar Christopher Musa ya ce Shugaba Ahmed Bola Tinubu bai ji daɗin samun raguwar man fetur ɗin da ake haƙowa ba, rahoton Politics Nigeria ya tabbatar.

Ya bayyana cewa raguwar haƙo man fetur ɗin ba alheri ba ne ga tattalin arziƙin ƙasar nan, inda ya umurci dukkan shugabannin hukumomin tsaro na Operation Niger Delta Safe da su tashi tsaye tare da dakatar da barazanar nan da makonni biyu.

Ya ce gwamnatin tarayya na son a riƙa haƙo gangar mai 2.5m a kowace rana, sannan ya kuma yi gargadin cewa duk wani jami’in tsaro da ya yi zagon ƙasa ga ƙoƙarin gwamnati na cimma hakan zai fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan

Ana batun zanga zanga, Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro wani umarni

Wane umarni ya ba jami'an tsaron?

"Na ba kwamandoji wa'adin mako biyu su kawo ƙarshen wannan ɓarnar. Babu canji kan kawo ƙarshen wannan ɓarnar cikin mako biyu."
"Ba wai kawai cikin ƙanƙanin lokaci za a cimma samar da ganga miliyan 2.5 ba, amma idan za mu dakatar da ayyukan ɓarayin, za mu samu cigaba sosai."

- Janar Christopher Musa

Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ba babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa umarnin daƙile satar mai da fasa bututun mai a yankin Niger Delta cikin ƙanƙanin lokaci.

Shugaba Tinubu ya ce wannan ɓarnar ta zama matsalar da ta shafi ƙasar da ya kamata a kawo ƙarshenta domin bunƙasa haƙo mai a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng