Tinubu Ya Ba JAMB Sabon Umarni Kan Adadin Shekarun Shiga Jami'o'i da Makarantu

Tinubu Ya Ba JAMB Sabon Umarni Kan Adadin Shekarun Shiga Jami'o'i da Makarantu

  • Yayin da ake kokarin neman gurbin karatu a manyan makarantun Najeriya, gwamnatin ta gindaya sharuda
  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa dole sai mutum ya kai shekaru 18 kafin samun gurbin shiga babbar makaranta a Najeriya
  • Gwamnatin ta ba da umarnin ne ga hukumar JAMB domin tabbatar da an bi tsarin yadda ya kamata ba tare da matsala ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwa kan adadin shekarun da ake bukata kafin shiga manyan makarantu.

Gwamnatin ta umarci hukumar kula da jarabawa ta JAMB da ta tabbatar sai masu shekaru 18 za a ba gurbin karatu a Jami'o'i.

Kara karanta wannan

Ndume: Daurawa ya nuna fargaba kan gwamnatin Tinubu, ya fadi illar haka gare su

Tinubu ya fitar da sanarwa kan adadin shekarun shiga manyan makarantu
Bola Tinubu ya umarci hukumar JAMB ta tabbatar da tsarin adadin shekarun shiga Jami'o'i nan take. Hoto: @DeeOneAyekooto.
Asali: Twitter

Tinubu ya kayyade shekarun shiga manyan makarantu

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman shi ya bayyana haka a yau Alhamis 18 ga watan Yulin 2024 a Abuja, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tahir Mamman ya ce ba ƴan ƙasa da shekara 18 gurbin karatu shi ke jawo wasu matsalolin a manyan makarantun kasar.

Ministan ya bukaci tabbatar da bin sabon umarnin domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a wannan ɓangare., Punch ta tattaro.

An yi tawaye ga umarnin gwamnatin Tinubu

Sai dai masu ruwa da tsaki a bangaren manyan makarantun da ke dakin da ake ganawar ba su amince da tsarin da aka kawo ba.

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede shi ya shiga tsakani domin kwantar da tarzomar da ta tashi yayin ganawar.

Wadanda suka ki amincewa da tsarin sun bayyana matsayarsu ne bayan Mamman ya ce ana tare a kan dokar, sai suka ce ba su tare da sabon umarnin.

Kara karanta wannan

"Tinubu na kokari, kar ku shiga zanga zanga," Minista ya lallabi jama'a

Ministan wanda ya nuna halin ko-in-kula da korafin nasu ya ci gaba da jawabi inda ya ke kokarin fadar musabbabin sanya dokar.

Tinubu ya naɗa shugabar ma'aikatan Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Didi Esther Walson-Jack, OON, a matsayin sabuwar shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya.

Bola Tinubu ya bayyana cewa naɗin na Misis Walson-Jack zai fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Agustan wannan shekara ta 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.