Abba Ya Karbo Filayen Makarantun da Ganduje ya Yanka Lokacin Yana Gwamnan Kano
- Gwamnatin Kano ta kwato filin makarantar kwalejin shari'a 'Legal' a Kano da tsohuwar gwamnati ta karbe
- Gwamna Abba Gida-Gida ya kwace filin ne bayan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yanka shi ga masu sha'awa
- Kwamishinan kasa da safayo na Kano, Alhaji AbdulJabbar Umar ya ce gwamnati na da hurumim yin hakan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kwace wasu filaye da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yanka. Filayen da gwamnatin ta kwace ya tashi daga kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar zuwa kwalejin shari'a ta Malam Aminu Kano.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa a jawabinsa, kwamishinan kasa da safayo na Kano, AbdulJabbar Umar ya ce gwamna na da ikon karbe filayen.
An maido wa makarantar fasaha filinta
Gwamnatin Kano ta mayar wa kwalejin shari'a da ke jihar filinta da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yanka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan kasa da safayo, Abduljabbar Umar ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya kara da cewa doka ta bawa gwamnati hurumin kwace filayen.
AbdulJabbar Umar ya kara da cewa binciken da su ka yi ya tabbatar da cewa an yanka filayen ba bisa ka'ida, wanda ya sanya su daukar matakin.
Gwamnatin Kano ta karbe filin Badume
Da ya ke karabar takardun filayen mataimaikinsa shugaban kwalejin shari'a, Dija Isa ya ce matakin zai habaka koyo da koyarwa a kwalejin.
A jawabinsa, Kwamishinan kasa da safayo ya ce gwamnati ta karbe iko da filin da gwamnatin Ganduje ta ba wa makarantar a Badume da ke Bichi.
Bayan karbe iko da filin kwalejin, gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta musanya masu da wani filin a Badume.
Za a raba taki ga manoma Kano
A wani labarin kun ji cewa mataimakin shugaban majalisa, Sanata Barau Jibrin ya dauki gabarar raba taki ga manoma da ke fadin jihar domin habaka noma.
Rabon na zuwa ne a lokacin da damuna ta kankama, inda Sanatan ya ce za a yi rabon torelolin taki 69 ga manoma da ke kananan hukumomin jihar 44.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng