Tsohon Shugaban Kasa Janar IBB ya Gano Hanyar Gyara Najeriya Daga Tushe

Tsohon Shugaban Kasa Janar IBB ya Gano Hanyar Gyara Najeriya Daga Tushe

  • Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce akwai bukatar dawo da darussan addini a makarantu
  • Ya shaida wa tawagar kungiyar kiristoci ta CAN reshen Neja cewa a shirye ya ke ya jagoranci wannan fafutukar
  • IBB ya ya nuna muhimmancin da darussan musulunci na IRK da na kirista, CRK ke da shi wajen saita tunanin jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger - Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bukaci dawo da darussan addini a makarantu. Ya fadi haka ne lokacin da tawagar kungiyar kiristoci reshen jihar Neja su ka ziyarce shi karkashin jagorancin Dr. Bulus Dauwa Yohanna.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki matakin inganta wutar lantarki a jihar Kano, Abba zai kashe N7.1bn

General Ibrahim Badamasi Babangida
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya nemi dawo da darussan addini makarantu Hoto: @Searchmediamx
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa tsohon shugaban na ganin ta hanyar dawo da koyar da darussan addinai a makarantu ne za a samu dawo da kasar nan cikin hayyacinta.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kara da cewa sai an dawo koya wa dalibai addinansu a makarantu kafin a samu canjin da ake bukata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zan jagoranci fafutukar darussan addini," IBB

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya ce zai jagoranci fafutukar dawo da darussan addini makarantun firamare da sakandaren.

Ya bayyana haka ne ga kungiyar kiristoci da su ka ziyarci gidansa da ke Minna, inda ya ce a lokacinsu an koya wa koya addininsa a makaranta.

Janar IBB ya ce dole ne a dawo da darussan addinin musulunci na IRK da na addinin kirista, CRK ga dalibai tun su na kanana, Jaridar Independent ta wallafa.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

"Sanin addini zai rage badala," IBB

Janar IBB ya bayyana cewa shayar da yara ilimin addini a wannan zamani da kafafen sada zumunta su ka yawaita zai rage badala.

Ya ce zai tattauna da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Neja, Umaru Bago wajen dawo da darussan.

Juyin mulki: IBB ya musanta gargadin Tinubu

A baya mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasar nan a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya musanta cewa ya gargadi Bola Tinubu.

An samu masu yada labarin cewa Babangida ya gargadi Tinubu a kan tsadar rayuwa a kasar nan, amma ya ce shi ba ya goyon bayan juyin mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.