Majalisa Ta Gayyaci Shugabannin Tsaro Kan Umurnin da Shugaba Tinubu Ya Ba da
- Majalisar wakilai ta gayyaci jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan umurnin noma da shugaba Bola Tinubu ya ba sojoji
- Ana sa ran cewa shugabannin tsaro za su yi gamsasshen bayani ga majalisar kan yadda za su cika umurnin shugaban kasar
- 'Dan majalisa mai lura da kwamitin tsaro, Babajimi Benson ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a jiya Talata a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci shugabannin tsaro su gurfana a gabanta domin yin bayani kan umurnin yin noma da Bola Tinubu ya ba su.
Majalisar ta bukaci shugabannin taron su gurfana a gabanta ne domin gamsar da ita kan yadda za su cika umurnin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa dan majalisa mai lura da harkokin tsaro ne ya fitar da sanarwar a jiya Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umurnin noma da Tinubu ya ba sojoji
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci sojoji da su rika noma filayen da suke da shi a fadin Najeriya, rahoton Tribune.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa hakan na cikin kokarin Bola Tinubu na samar da abinci da inganta tsaro a Najeriya.
Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro
Majalisar wakilai ta gayyaci ministan tsaro, Badaru Abubakar da babban hafsun tsaro Janar Christopher Musa.
Majalisar ta ce za su mata bayani ne kan yadda za su cika umurnin kasancewar su ne masu samar da tsaro a Najeriya.
Yaushe za su gurfana a majalisa?
Shugaban kwamitin tsaro a majalisar wakilai, Babajimi Benson ya ce a ranar Litinin mai zuwa ne ake tsammanin za su gurfana a gaban majalisar.
Babajimi Benson ya bayyana cewa tsarin yin noma ga sojoji da shugaban kasa ya kawo abu ne mai kyau da zai inganta tsaro a Najeriya.
An raba taki ga manoma a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa a yayin da damunar bana ta kankama a Arewa, an fara rabon taki ga manoma a kananan hukumomin jihar Kano.
Sanata Barau Jibrin ne ya kaddamar da fara rabon takin ga manoma a fadin jihar Kano a jiya Talata, 16 ga watan Yuli.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng