'Yan Sanda Sun Cafke Sufeto Bisa Zargin Fashi da Satar Mota
- Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da cafke wani jami'inta da ake zargi da fashi bayan an gano shi motar sata
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Williams Ovye-Aya ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a jihar
- Kakakin ya ce an gano motar lokacin da ake kokarin sauya mata launi, bayan an sauya mata lamba da yi mata takadu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kogi - Rundunar 'yan sandan Kogi ta tabbatar da cafke wani jami'inta, Sufeto Aminu Mohammed bisa zargin fashi da satar mota.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Williams Ovye-Aya ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce tuni su ka cika hannunsu da Sufeton.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sufeto Aminu Mohammed na aiki ne da bangaren kula da miyagun ayyuka na rundunar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi Sufeto da satar mota
Rundunar yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa ana zargin Sufeto Aminu Mohammed da satar mota tare da kokarin sauya mata kamanni.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa an tsinci motar sata a garejin mai gyara wa Sufeton mota inda a nan ne rahoto ya iso garesu.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Williams Ovye-Aya ya ce wadanda su ka samu labarin sace motar ne su ka shaida wa jami'an tsaro batun.
Yadda aka gano motar
SP Williams Ovye-Aya ya bayyana cewa bayan rahoton gano motar ne jami'ai su ka ziyarci garejin, inda su ka yi ram da mai gyaran motar.
Bayan an gudanar da bincike ne sai mai gyaran ya bayyana cewa dan sanda Aminu ne ya kawo masa gyaranta.
Tuni aka sauya lambar motar zuwa ta Abuja, sannan an sauya lokacin da aka sayi motar zuwa 2020.
An kama dan sandan bogi
A baya mun kawo labarin cewa rundunar 'yan sandan Legas ta damke wani dan sandan bogi bayan an fara zarginsa da damfarar jama'a.
Rundunar ta bayyana cewa tuni ta dauki mataki kan matashin mai suna Charles Chukwudi domin dakile ra'ayin matasa masu son aikata haka.
Asali: Legit.ng