Ana Shirin Zanga Zanga, NLC Ta Turawa Majalisa Gargadin Tsaida Ayyuka Cak na Kwanaki 30

Ana Shirin Zanga Zanga, NLC Ta Turawa Majalisa Gargadin Tsaida Ayyuka Cak na Kwanaki 30

  • A yayin da matasan Najeriya ke yin barazanar shiga zanga-zanga a fadin kasar nan, kungiyar kwadago ta tura sabon sako ga majalisa
  • Kungiyar kwadago ta gargadi majalisa kan shirin da Bola Tinubu yake na kai musu kudurin mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya
  • Shugaban yan kwadago ya ce idan majalisa ba ta yi abin da ya kamata ba za su dauki matakin dakatar da lamura cak a faɗin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta yi gargadi ga majalisar tarayya a lokacin da Bola Tinubu ke shirin mika kudurin mafi ƙarancin albashi.

Kungiyar NLC ta bayyana cewa dole yan majalisu su taka rawa mai kyau wajen ganin ma'aikata sun samu albashi mai tsoka.

Kara karanta wannan

AYCF: Kungiya ta fadi hanyoyin da matasa za su bi wajen yin zanga zanga lafiya

Yan kwadago
Yan kwadago na shirin shiga yajin aiki. Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

Jaridar the Guardian ta ruwaito cewa shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero ne ya yi kiran a jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da zai sa NLC rufe kasa

Shugaban kungiyar kwadago ta bayyana cewa idan majalisa ta kawo tsaiko wajen samar da mafi ƙarancin albashi mai tsoka, za su kulle Najeriya baki daya.

Joe Ajaero ya ce za su tsayar da ayyuka cak a Najeriya na tsawon wata daya domin nuna fushin ma'aikatan Najeriya.

Shugaban ya ce wannan matakin ya zama dole duba da yadda yan majalisa da gwamnonin jihohi ba su daukan ma'aikata a bakin komai.

NLC: 'A rage albashin yan majalisa'

Kungiyar kwadago ta bukaci a rage albashi da alawus na yan majalisun Najeriya lura da yadda ake kukar rashin kuɗi a kasar, rahoton Punch.

Shugaban yan kwadago ya koka kan cewa kudin da suke kashewa ya wuce kima saboda haka ya bukaci a dawo da su kan mafi ƙarancin albashi.

Kara karanta wannan

A karshe: Tinubu ya yarda akwai yunwa a Najeriya, ya dauki sabon mataki

Joe Ajaero ya bayyana cewa dukkan abin da ya shafi walwalar ma'ikata za su rika ba shi muhimmanci sosai har sai sun kwaci hakkinsu.

AYCF ta shawarci masu zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi kira na musamman ga matasa da ke shirin fita zanga zanga a Najeriya.

Kungiyar ta ba matasan shawara kan yadda ya kamata zanga zangar ta kasance domin kaucewa barkewar rikici a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng