Sabon Rikici Ya Kunno Kai a PDP, Kotu Ta Haramtawa Jam’iyya Gudanar da Babban Taro

Sabon Rikici Ya Kunno Kai a PDP, Kotu Ta Haramtawa Jam’iyya Gudanar da Babban Taro

  • Wata babbar kotun Ribas da ke zamanta a Fatakwal, babban birnin jihar ta hana jam’iyyar PDP gudanar da taronta a jihar
  • Alkalin kotun, Mai shari’a Sobere Biambo, ya bayar da umarnin wucin gadi na hana taron PDP da aka shirya yi a ranar 27 ga Yuli
  • Kotun ta bayar da umarnin ne a wata kara mai lamba PHC/2282/CS/2024 da Hon. David Chiinedu Omereji da mutum 10 suka shigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Rikicin jam’iyyar PDP a jihar Ribas ya kara kamari, biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke na hana shugabannin jam’iyyar gudanar da babban taronta.

Babbar kotun da ke zamanta a Fatakwal, babban birnin jihar, ta hana jam’iyyar gudanar da taron da ta shirya yi a ranar 27 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Kamar al'amara: Yadda barawo ya yaudari direban kabu-kabu da farfesa, ya sace motarsa

Kotu ta yi hukuncin kan taron jam'iyyar PDP a jihar Rivers
Kotu ta dakatar da Jam'iyyar PDP daga gudanar da taronta a jihar Rivers. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa kotun ta bayar da umarnin ne a karar da aka shigar kan PDP reshen jihar, shugaban PDP na kasa, sakataren kudi da kuma sakataren jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta haramtawa jam'iyyar PDP yin taro

Alkalin kotun, Mai shari’a Sobere Biambo, ya bayar da umarnin hukuncin wucin gadi na hana wadanda ake kara shirya taron jam'iyyar har sai an yanke hukunci.

Kotun ta kuma dakatar da jam'iyyar PDP daga kara wa’adin shugabannin gunduma, kanananan hukumomi da na jihar wanda ya kare tun tuni, inji rahoton The Punch.

Mai shari'a Sobere Biambo ya dage sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Yuli inda zai saurari wata bukatar da aka riga aka shigar kan shari'ar.

Su wa suka shigar da PDP kara?

Kotun ta bayar da umarnin ne a wata kara mai lamba PHC/2282/CS/2024 da Hon. David Chiinedu Omereji, Hon. Prince Solomon Eke, Isodoye Tobin da Goddy Manfred Pepple suka shigar.

Kara karanta wannan

Harka ta lalace: Mai aukuwa ta auku, an ba 'yan kasar waje wa'adin barin Sudan cikin gaggawa

Sauran sun hada da Okiah Precious Chigozirim, Hon. Orolosama Peter Amachree, Goodfriday Nweke, Alfred Letam, Hon. Wechie Ndubisi Raymond, Misis Erebie Michael da Hon. Ogenma Idalunimulu.

An nemi a tube shugabar matan PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu matan PDP sun gudanar da zazzafan zanga zanga a birnin tarayya Abuja saboda rashin jin dadin wasu lamuran jami'yyar.

Matan sun gudanar da zanga zangar ne domin nuna kin amincewa da jagorancin shugabar matan jami'yyar ta kasa, Amina Darasimin D. Bryhm.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.