Ana Batun Zanga Zanga, Shugaba Tinubu Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Umarni
- Shugaban ƙasan Najeriya Bola Tinubu ya nuna damuwarsa kan ayyukan masu satar mai da fasa bututun mai a yankin Neja Delta
- Shugaba Tinubu ya umarci babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, da ya kawo ƙarshen matsalar cikin lokaci ƙanƙani
- Janar Christopher Musa ya sha alwashin cewa jami'an tsaro za su kawo ƙarshen matsalar da ake fama da ita a yankin mai arziƙin man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ba babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa umarnin daƙile satar mai da fasa bututun mai a yankin Niger Delta cikin ƙanƙanin lokaci.
Shugaba Tinubu ya ce wannan ɓarnar ta zama matsalar da ta shafi ƙasar da ya kamata a kawo ƙarshenta domin bunƙasa haƙo mai a ƙasar nan.
Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, yayin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar tsaro dake Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mele Kyari ya gana da manema labaran ne bayan wani taron shugabannin hukumomin tsaro da na leƙen asiri da babban hafsan tsaron ya kira, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Wane umarni Tinubu ya ba jami'an tsaro?
Shugaban na NNPC, ya ce samun daidaiton tattalin arziƙin da ake so ba zai taɓa yiwuwa ba, ba tare da daƙile satar man fetur da sauran laifuffuka a yankin Neja Delta ba.
"Mun zo nan ne domin tattaunawa da babban hafsan tsaro na ƙasa bisa umarnin shugaban ƙasa. Shugaban ƙasa ya umarce shi da ya shawo kan rikicin da muke fama da shi a yankin Neja Delta."
"Satar mai da fasa bututun mai ya zama babbar matsala ga ƙasa, shugaban ƙasa ya umarci babban hafsan tsaro ya daƙile hakan cikin ƙanƙanin lokaci."
- Mele Kyari
Babban hafsan tsaro ya sha alwashi
Babban hafsan tsaron, Christopher Musa, ya sha alwashin cewa sojoji da sauran hukumomin tsaro za su kawar da duk wasu ayyukan ɓarna da sauran miyagun ayyuka a yankin Neja Delta.
Christopher Musa ya ce lokaci ya yi da za a kawar da matsalar domin ci gaban ƙasar nan.
Tinubu ya yi ta'aziyyar ɗan majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓun Chikun/Kajuru na jihar Kaduna a majalisar wakilai, Honorabul Ekene Adams.
Shugaban ƙasan ya jajantawa majalisar dokokin tarayya da gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan rashin na ɗan majalisar da aka yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng