Ana Tsaka da Cin Kwakwa, Gwamna Zai Ba Ma'aikata N45,000 Domin Rage Raɗaɗin Kunci

Ana Tsaka da Cin Kwakwa, Gwamna Zai Ba Ma'aikata N45,000 Domin Rage Raɗaɗin Kunci

  • Ma'aikata a jihar Abia za su sha jar miya yayin da gwamnati ta ware N45,000 kyauta domin rage musu halin ƙunci
  • Gwamnatin jihar ta ware kudin ne domin biyan ma'aikatan N15,000 har na tsawon watanni uku saboda mawuyacin hali da ake ciki
  • Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikaci da ke aiki a ma'aikatar gwamnatin jihar Gombe kan wannan abin alheri da Gwamna Otti ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Yayin da ake cikin wani irin yanayi a Najeriya, gwamnatin jihar Abia ta sharewa ma'aikata hawaye.

Gwamnatin jihar ta amince da biyan ma'aikatan jihar N15,000 tsawon watanni uku wanda zai kama N45,000 domin rage musu radadi.

Kara karanta wannan

"Ban ce zan biya N80,000 ba," Gwamna ya musanta rahoton zai yi karin albashi

Gwamna ya amince da ba ma'aikata N45,0000 saboda halin kunci
Gwamna Alex Otti na Abia zai ba ma'aikata N45,000 na rage radadi. Hoto: Alex Otti.
Asali: Facebook

Gwamna zai gwangwaje ma'aikata da N45,000

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Prince Okey Kanu ya fitar a jiya Litinin 15 ga watan Yulin 2024, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okey Kanu ya ce ma'aikatan za su samu N15,000 tsawon watanni uku saboda rage raɗaɗin da ake ciki yanzu.

Ya ce Gwamna Alex Otti ya himmatu wurin inganta rayuwar ma'aikatan jihar inda ya ce za a fara biyansu kudin hutu.

Gwamnan Abia ya yi alkawura ga ma'aikata

"Saboda yadda gwamnatin Abia ke son tallafawa ma'aikata, ta amince da biyan N45,000 amma na tsawon watanni uku za a biya N15,000."
"Mun gaji tarin kudaden alawus na ma'aikata da ake biya lokacin da suke hutu."
"Ganin yadda gwamnan Abia ya himmatu wurin inganta rayuwar ma'aikata, za a fara biyan ma'aikaci duk lokacin da ya tafi hutu a wurin aiki."

Kara karanta wannan

Kano: Sarki Sanusi II ya koka kan halin kunci da ake ciki, ya yabawa gwamnatin Abba

- Prince Okey Kanu

Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikaci da ke aiki a ma'aikatar gwamnatin jihar Gombe kan wannan abin alheri da Gwamna Otti ya yi.

Umar Abdulkadir ya ce a Gombe har yanzu Gwamna Inuwa Yahaya yana ci gaba da biyansu kudin rage radadin cire tallafi.

"Kamar yadda gwamnan ya yi alkawarin biyan N10,000, har yanzu yana ci gaba da biya."

- Umar Abdulkadir

Sanwo-Olu ya gwangwaje matasa da kyautar N100,000

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi abin alheri ga matasa masu bautar ƙasa da aka tura jihar Lagos.

Sanwo-Olu ya ba kowane matashi mai bautar kass kyautar N100,000 domin su yi walwala ganin halin kunci da ake ciki a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.