"Raba Mudun Shinkafa ba Zai Magance Yunwa ba" Kungiyoyi sun Kawowa Tinubu Mafita

"Raba Mudun Shinkafa ba Zai Magance Yunwa ba" Kungiyoyi sun Kawowa Tinubu Mafita

  • Kungiyoyi sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan yunkurin gwamnati na raba torelolin shinkafa ga jihohin kasar nan
  • Shugabar kungiyar manoma mata ta SWOFAN, Fatima Gunmi ta ce bai kamata ayi rabon ba, da dai an bunkasa noman cikin gida
  • Ita kuma Kungiyar rumbun abinci ta shaida wa Legit cewa akwai bukatar a tabbata an bude iyakoki domin shigo da abinci zai karya farashin sa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano - Kungiyar mata manoma ta SWOFAN ta bayyana cewa rabon shinkafa kwano ɗai-ɗai ba zai magance yunwa a kasar nan. Kungiyar ta yi martani kan iƙirarin gwamnatin tarayya na aika wa da tireloli 20 ga kowacce jiha domin raba wa ga talakawa.

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta fatattaki shugabanta saboda goyon bayan shirya zanga zanga

Bola Tinubu
Kungiyoyi sun ce rabon shinkafa ba zai magance yunwa ba Hoto: Ajuri Ngelale/Bloomberg
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugabar kungiyar, Fatima Gunmi ta ce matakin bunkasa noma ya kamata gwamnati ta dauka.

A makon nan ne gwamnatin tarayya ta ce za ta tura tirelolin shinkafa ga jihohin kasar nan 36, Premium Times ta wallafa labarin.

"Gwamnati ta tallafa wa manoma," SWOFAN

Kungiyar mata manoma shinkafa ta ce idan har gwamnati na son magance yunwa, ta taimaka wa manoman cikin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar kungiyar, Fatima Gunmi ta ce sun samu labarin wasu 'yan majalisa na raba taki da sauran kayan amfanin gona, amma ba ya karaso wa ga manoman.

"A shigo da shinkafa," Kungiyar rumbun abinci

Kungiyar rumbun abinci da ke tallafa wa mabukata a Kano ta ce shigo da abinci zai taimaka wajen rage yunwa.

Kungiyar na da ra'ayin rabon abinci da gwamnatin tarayya ke shirin yi ba zai zama mafita ba.

Kara karanta wannan

Ana kokarin dakatar da Tinubu daga bude iyakoki, shugaban AfDB ya kawo shawara

Shugaban kungiyar, Muhammad Sani Garba ya shaida wa Legit cewa idan aka rika shigo wa da abinci, 'yan kasuwar cikin gida za su sayar da na su da sauki.

Gwamnati za ta fara rabon abinci

A baya mun ruwaito cewa halin yunwa da kasar nan ke ciki ya sa gwamnatin tarayya sanya ranar fara raba tallafin abinci.

Gwamnan jihar Neja, Ibrahim Bago ya bayyana cewa za a fara rabon hatsin ta jiharsa a yunkurin gwamnati na taimaka wa 'yan kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.