Gwamnan Katsina Ya Bayyana Hanyar da Yake Bi Wajen Samar da Tsaro

Gwamnan Katsina Ya Bayyana Hanyar da Yake Bi Wajen Samar da Tsaro

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi bayani na musamman kan harkokin sana'a ga al'ummar jihar
  • Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana irin ayyukan da gwamnatinsa ta samar domin bunkasa sana'o'i a jihar
  • Ya kuma fadi rawar da koyon sana'a za ta taka wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Katsina da kewaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayyana hanyar da suka dauka wajen samar da zaman lafiya a jihar.

Dikko Umaru Radda ya yi bayanin ne a jiya Litinin yayin murnar ranar sana'ar hannu ta duniya da ake yi duk ranar 15 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya ɗauki muhimmin mataki na kawo ƙarshen masu ƙwacen waya

Gwamna Radda
Gwamnatin Katsina za ta koyar da sana'o'i domin samar da tsaro. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da gwamnan ya yi ne cikin sakon da jami'in yada labaran jihar, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyar samar da tsaro a Katsina

A yayin taron, gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa koyon sana'a ita ce hanyar da suka dauka domin tabbatar da zaman lafiya a Katsina.

Gwamnan ya fadi haka ne kasancewar majalisar dinkin duniya ta alaƙanta taken ranar sana'o'i ta duniya a bana da zaman lafiya.

Koyawa matasa sana'a a Katsina

A bangaren koyon sana'o'i gwamna Dikko Radda tabbatar cewa sun ba matasa muhimmanci sosai.

Gwamnan ya ce saboda koyawa matasa sana'o'i ne suka inganta cibiyar koyon sana'a ta jihar Katsina, rahoton Punch.

Ya kuma bayyana cewa sun yi haɗaka da kungiyoyi da ma'aikatau da dama wajen ganin an ba matasa dama sun koyi sana'o'i a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Ruwa ya ruguza gidaje da rumbunan abinci a Arewa, mutane sun shiga tasko

Kiran gwamnan Katsina ga kungiyoyi

A karshe, gwamna Dikko Umaru Radda ya yi kira ga kungiyoyi da masu ruwa da tsaki su shigo a hada kai da su wajen samar da sana'o'i a jihar.

Ya jaddada cewa wannar ita ce hanyar da suka dauka domin samar da jiha mai aminci da samar da matasa da za su habaka jihar.

Katsina: Kungiya ta yi kira ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar dattawan jihar Katsina ta bayyana takaicin yadda gwamnatin Bola Tinubu ke wasarere da rayukan 'yan kasa.

Kungiyar, ta bakin sakatarenta Malam Aliyu Mohammed ta zargi gwamnati da kokarin kawo auren jinsi da dangoginsa ga 'yan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng