Zaman lafiya ya samu: Mutane 2,027 sun koma gidajensu a jihar Katsina

Zaman lafiya ya samu: Mutane 2,027 sun koma gidajensu a jihar Katsina

- Mutane da yawan gaske sun koma gidajensu daga sansanin 'yan gudun hijira na Jibiya

- Sun koma kauyukansun a jiya Litinin, bayan sun samu tsaro daga wajen jami'an tsaro na hadin guiwa

- A makon da ya gabata ne dai aka kaiwa kauyukansu guda hudu hari, inda 'yan bindiga suka dinga cin zarafin su

Kimanin mutum 2,027 ne suka koma kauyukansu guda hudu a karamar hukumar Jibya dake jihar Katsina.

Mutanen dai an tilasta su suka bar gidajensu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai makon da ya gabata, inda a jiya Litinin duka suka koma gidajensu.

Gwamnatin jihar ce ta bukaci mutanen da su koma muhallansu.

Mutanen da suka koma Jibiya da zama makon da ya gabata a ranar Alhamis, sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai musu kauyensun, an basu masauki a makarantar firamare ta Jibiya.

Zaman lafiya ya samu: Mutane 2,027 sun koma gidajensu a jihar Katsina
Zaman lafiya ya samu: Mutane 2,027 sun koma gidajensu a jihar Katsina
Source: Twitter

Bincike ya nuna cewa mutanen sun fito daga kauyen Tsamben Tsauni, Tsamben Kotumbo, Tsamben Radi da kuma Tsamben Zango.

Daga baya an gano cewa 'yan bindigar sun shiga kauyukan makon da ya gabata ranar Talata da Laraba, inda suka cin zarafin mutanen kauyukan.

A cewar Mai Garin Tsamben Tsauni, Ibrahim Ali-Magarin, 'yan bindigar sun yiwa mata da yawa fyade suka yiwa maza da yawa mugayen raunika saboda sun kasa basu kudade.

KU KARANTA: Rikici ya barke a wajen biki, bayan 'yan uwan miji sun gano cewa amaryar da zai aura tana da miji

Ali-Magarin, ya ce 'yan bindigar sun sace mata guda biyu, sannan sun gudu da akuyoyi 170, sun kuma kwashi kayan abinci da kuma wasu abubuwa daban-daban a kauyen.

Ya ce: "Dole ta sanya muka gudu muka bar kauyen da muka ga 'yan bindigar sun kawo mana hari har sau biyu cikin mako guda. Amma mun gode Allah da gwamnatin jiha wajen saka hannu a lamarin har muka samu damar dawowa gidajen mu yau Litinin.

An gano cewa rundunar hadin guiwa ta sojoji da 'yan sanda ne suka raka mutanen gidajensu.

Shugaban 'yan gudun hijira na Jibiya, Gide Dahiru, wanda ya ga lokacin da lamarin ya faru, yayin da mutanen ke komawa kauyukansu, ya ce an umarci jami'an tsaron da su tsaya a garin domin tabbatar da tsaro ga mutanen yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel