Gwamnatin Tarayyah za ta koyar da mata 2,800 sana'o'i a jihar Kano
- Gwamnatin Tarayyah za ta koyar da mutane 4000 sana'oi daban- daban a jihar Kano
- Mutane 2,800 cikin 4000 da su amfana da shirin mata ne
- An ware ma matan gurbin mai tsoka ne saboda muhimiyar gudun mawar da suke bayar wa wajen cigaban al'umma
A karkashin shirin gwamnatin Tarayyah na samar da ayyuka 76,400 a fadin kasar nan, hukumar samar da ayyuka na kasa (NDE) za ta koyar da mutane 4000 sana'o'i daban-daban a jihar ta Kano.
A jawabin da ya yi a wajen taron kadamar ta shirin a sakatariyar hukumar ta NDE a Kano, Jagoran shirin na jihar, Iliyasu Ahmed ya bayyana cewa 70% na sana'o'in za'a koyar da mata ne wato 2,800 kenan, maza kuma 1,200.
DUBA WANNAN: Zaben 2019: PDP ta za ta tsayar da dan takara mafi inganci daga Arewa - Walid
Kamar yadda ya ce, an bayar da kaso mai tsoka ga matan ne saboda muhimmiyar rawar da su ke takawa wajen ciyar da al'umma gaba. Ya ce za'a basu horo sannan kuma a basu tallafi domin su cigaba da sana'o'in kuma su tallafawa kansu.
"Kashi saba'in na sana'o'in da za'a koyar a jihar Kano zai tafi zuwa ga mata ne, za'a koyar da su sana'o'in kayan shafe-shafe ne kuma a ba su tallafi da za su kafa ta su sana'ar. Sauran wadanda za su amfana da shirin kuma maza ne da za'a bawa horo kan sana'o'i daban-daban." Inji shi
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng